Home / Big News / An Kone Mutane 16 Har Lahira A Kauyen Kaduna

An Kone Mutane 16 Har Lahira A Kauyen Kaduna

A Kalla mutane 16 ne aka tabbatar da mutuwarsu a kauyen Bakali da ke masarautar Fatika cikin karamar hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
Wannan lamari dai kamar yadda majiyar mu ta tabbatar mana cewa ya faru ne sakamakon irin mamayar da yan bindiga suka yi wa kauyen baki daya inda suka kulle wadansu mutane a cikin daki suka kunna wuta nan take.
 Yan bindigar dai sun shiga kauyen ne da misalin karfe 4 na Yamma suka kunna wa buhuhunan Hatsi, Babura tare ababen hawa da wuta a kauyen baki daya.
Kamar yadda majiyar mu ta shaida mana cewa yan bindigar sun kulle mutane 16 a cikin daki da suka kasance yan gida daya suka kunna masu wuta baki daya.
Daya daga cikin mutanen kauyen mai suna Alhaji Sani Bakali, ya tabbatarwa wakilinmu faruwar lamarin inda ya ce sama da yan bindiga dari ne suka mamaye kauyen suka cutar da jama’a.
Zamu ci gaba da kawo maku rahoton yadda al’amura ke tafiya a kauyen nan gaba kadan.

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.