A kokarin al’umma musamman marasa galihu sun samu damar tsayawa da kafafunsu yasa Muryar darika koyawa mutane dari 660 sana’o’in da za su dogara da kansu.
Bisa wannan dalilin ne ma yasa zababen gwamnan Jihar Katsana Dr Dikko Umar Rada ya yabawa Muryar Darikar Tijjaniyya Funtuwa ,bisa kokarinta na koyawa mutane dari shida da sitin Sana’oi dan dogara da kansu.
Dr Dikko Umar Rada, da ya samu wakilin Abdurahaman Nasir,a wajan raton ya bayyyana cewa,wannan shi ne kudirin zababben Gwamna Rada,da zarar ya shiga fadar gidan Gwamnatin Jihar Katsina.
Zabeben gwamnan Rada ya tabbar da cewa,zai mara ma wannan shirin baya dan ganin kudirin su ya cika na samarwa alumma sana’aryi dan dogaro da kai batare da jiran aikin gwamnatiba.
Shugaban sashen koya sana’oin Malam Nuhu Kabir ,ya bayyyana cewa, Wannan bikin yaye daliban da Muryar Darika ta koyawa Sana’oi, ba shi ne na farko ba dan a watannin baya mun horar da mutane 210,yau kuma gashi mun horar da mutane dari shida da sittin da shida Sana’oi daban-daban dan dogara kai da ciyar da al’umma gaba”, injii Malam Nuhu”.
“Malam Nuhu Kabir ya kuma kara da cewa,wadanda suka amfana da wannan horan Sana’oi ,sun hada da Marayu, Marasa karfi ,Mata da matasa kuma kowane shi ne ya zabar makansa sana’ar da yake da shi’awa akanta .
Kuma yanzu haka Sana’oi goma shabiyar ne kala daban daban muka koyawa mutane ,wadanda suka hada da Manyan Shafawa, Man gyaran Fata ,Sabolin wanka da na Wanki,Man kitso ,Man Humra da kuma maganin gargajiya da dai sauran su,inji Shugaban Malam Nuhu Kabir.
Kalifa Ali Saidu Alti da Limana Abdurahaman ne suka jagoranci taron a matsiyin su na jogogin Muryar Darika Tijaniya da ke Karamar hukumar ta Funtua.