Home / Labarai / An Nada Bello Kagara Sarkin Yakin Danejin Katsina

An Nada Bello Kagara Sarkin Yakin Danejin Katsina

An Nada Bello Kagara Sarkin Yakin Danejin Katsina
Mustapha Imrana Abdullahi
Bayan samun amincewar Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ga Danejin Katsina Hakimin Mahuta Alhaji Bello Abdulkadir Yammama na ya nada Alhaji Bello Kagara tare da wadansu mutane sha shida (16) sarautun gargajiya daban daban domin nuna gamsuwa da alfahari da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ciyar da yankin,Jiha da kasa baki daya gaba.
A ranar Lahadi 3 ga watan Afrilu ne garin Mahuta da Kagara suka karbi bakuncin dimbin al’ummar da yawansu ya wuce misali daga fadin duniya baki daya.
Bikin nadin dai ya hada har da na dan majalisar wakilai Alhaji Babangida Talau da tsohon babban Sakatare tare da wadansu dimbin fitattun mutanen da suka bayar da gudunmawarsu domin ciyar da al’umma gaba.
Wadanda Hakimin Mahuta Alhaji Bello Abdulkadir Yammama ya nada dai sun hada da
1. Alhaji Tijjani Ahmad – Sarkin Fulanin Daneji.
2. Alhaji Babangida Ibrahim – Khadimul Islam na Daneji.
3. Alhaji Bello Hussaini – Sarkin Yakin Daneji
4. Alhaji Mahe Abubakar – Wakilin Daneji
5. Labiru Musa Kafur – Talban Daneji
6. Shehu Abdulkadir – Sallaman Daneji
7. Alhaji Sabi’u Sa’idu – Sardaunan Daneji
8. Abdulhamidu Sale – Tafidan Daneji
9. Alhaji Ummar Abdulkadir – Chiroman Daneji.
10. ABBA Abdulkadir – Sarkin Dawakin tsakar gida
11. Abubakar Abba Kabir – Kaigaman Daneji.
12. Usman Mansir – Wazirin Daneji.
13. Kabir Abdullahi – Jagaban Daneji.
14. Dokta Nura Husaini – Wazirin Maganin Daneji
15. Abdulmumini Dahiru – Dan burman Daneji
16. Umar Abubakar – Dallatun Daneji
17. Abdul Malik Haruna – Sarkin Samarin Daneji.
An dai yi wannan nadin ne a cikin garin Mahuta mazaunin sarautar Danejin Katsina Hakimin Mahuta, kuma hakimai Dagatai da sauran dimbin jama’a duk sun samu halarta ciki har da Hakimin Malumfashi za dai mu ci gaba da kawo maku cikakken rahoton da ya hada da hotuna da bidiyo a nan gaba kadan tare da jawaban yan uwa da abokan Alhaji Bello Kagara Sarkin yakin Danejin Katsina Hakimin Mahuta.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.