Home / Labarai / An Nada Farfesa Kailani Muhammad Sarautar Okuku Ogu Na Kasar Igbo

An Nada Farfesa Kailani Muhammad Sarautar Okuku Ogu Na Kasar Igbo

 

Daga Imrana Abdullahi

Sakamakon kokarin taimakawa jama’a da aikin tukuru ya sa al’ummar Ibgo sula nada Farfesa Injiniya Kailani Muhammad sarautar Okuku Ogu na kasar Igno wato mai taimakon al’umma a koda yaushe Dare da rana safiya da maraice da nufin samun ingantacciyar al’ummar da za ta dogara da kanta.

Kamar dai yadda masu yin huldar arziki da Farfesa Kailani Muhammad suka Sani kuma za su iya bayar da sheda a ko’ina kuma a gaban kowa cewa shi mutum ne da a kullum abin hannunsa komai yawansa duk na jama’a ne domin Farfesa Kailani Muhammad Mutum ne wanda ba ya cin abinci ko abin sha shi kadai dole a kullum sai tare da jama’a kuma da zarar ya fito daga gida ya dinga yin kyauta ga jama’a kenan Maza da Mata.
Kai shi ne mutumin da ke tafiya neman abin duniya don kawai ya samawa jama’a sauki a cikin gudanar da harkokin rayuwarsu domin Farfesa Kailani Muhammad ne ya ta fi Abuja daga Kaduna ya zamowa jama’a aikin inganta wutar lantarki da ke Unguwar Rigasa kuma an zo an yi wannan aiki inda aka cike Fala- falan turken wutar Lantarki aka Sanya na zamani tare da wayoyin masu kyau masu inganci banda na’urar rarraba wutar lantarkin da aka Sanya duk domin jama’a su samu sauki rayuwarsu ta inganta.
Mutim ne da zaka tarar da gidansa ba masaka tsinke tun daga Kofar gidan har ko’ina da ko’ina duk mutane ne da hidimar arziki ta kawo su kuma za su ci su kuma sha cikin irin arzikin da Allah ya yi wa Farfesa Kailani Muhammad cikakken Injiniya masan8n harkokin Matatar Man fetur a tarayyar Najeriya.
A ganina Visa irin wadannan dalilai ne yasa al’ummar Igbo da ke zaune a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya suka ga dacewa su Karrama Farfesa Kailani Abubakar Muhammad da babbar Sarautar Okuku Ogu wato mai taimakon al’umma, wanda hakan ya farantawa duk masoya, yan uwa da abokan arziki tare da masu son kasa da al’ummarta rai domin karramawa ce ta sarauta da aka yi ta a wurin da ta dace.
Da yake jawabi ga manema labarai Farfesa Kailani Abubakar Muhammad ya shaida masu cikakken farin ciki da jindadinsa bisa yadda al’ummar Igbo suka ga dacewar sa da wannan sarautar ta mai taimakon al’umma, abin da ya bayyana da cewa a da can ana ganin kamar su al’ummar Igbo ba su san yin cudanya da jama’a sai dai su kawai don haka wannan ya nuna cewa ba haka lamarin yake ba.
Sai dai Farfesa Kailani Muhammad ya yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya waiwayo baya ya kuma duba yayan kungiyarsu da suka yi fafutukar kafa wannan Gwannatin ksancewar suna da dukkan mutane a ko’ina a fadin tarayyar Najeriya domin suna da jama’a a kowa ne akwatin zabe da ke kasar kuma duk sun bayar da gudunmawarsu har an kafa Gwamnati karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa.
“Amma abin mamaki shi ne har yanzu ba a nada kowa ba a matsayin wani mukami a tarayyar Najeriya misamman a Gwamnatin tsakiya da shugaba Bola A Tinubu ke yi wa jagoranci don haka suke kira da babbar murya a hanzarta yin hakan saboda yayan kungiyar ta su da suka yi fafutuka sun dace a ba su kujerun mukamai na gwamnati.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.