Home / Labarai / An Nada Sale Musa Kwankwaso Hakimin Madobi

An Nada Sale Musa Kwankwaso Hakimin Madobi

An Nada Sale Musa Kwankwaso Hakimin Madobi
Mustapha Imrana Abdullahi
Mai martaba Sarkin Karaye Alhaji Dokta Ibrahim Abubakar III ya bayyana nadin Alhaji Sale Musa Kwankwaso da ake yi wa lakabi da (Baba) a matsayin Hakimin Madobi.
 Sabon Hakimin Madobin shi ne Dagacin Garin Kwankwaso kuma ya dade yana yi wa wannan gari na su hidima, wanda hakan ta sa cancantarsa a matsayin magajin mahaifin sa.
Dimbin jama’a dai sun bayyana wannan sabon nadin sarauta a matsayin karamcin da aka yi wa gidan marigayi Mahaifin tsohon Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso.
Za’ a mika wa Gwamna Ganduje a rubuce wannan sabon nadi domin sahalewarsa. Muna taya sabon Makaman Karaye kuma Hakimin Madobi murnar wannan sabon matsayi.

About andiya

Check Also

An Yi Walimar Taya Soja Abdurrahman Abdullahi Shinkafi Murnar Zama 2nd Lieutenant A Kaduna

Daga Imrana Andullahi Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Mahmuda Aliyu Shinkafi, yi wa Allah godiya ya …

Leave a Reply

Your email address will not be published.