Home / Uncategorized / Kwamishinan Muhalli Hamza Sule Faskari Ya Ceto Rayuwar Wani Yaro

Kwamishinan Muhalli Hamza Sule Faskari Ya Ceto Rayuwar Wani Yaro

Kwamishinan Muhalli Hamza Sule Faskari Ya Ceto Rayuwar Wani Yaro

Mustapha Imrana Abdullahi
Kwamishinan ma’aikatar kula da muhalli na Jihar Katsina honarabul Hamza Sule Faskari, cikin ikon Allah ya samu nasarar ceton rayuwar wani bawan Allah da ke fama da karaya a kashin bayansa.

    Yaron da ke fama da karaya a bayansa mai suna Mu’azu Lawal
Shi dai yaron kamar yadda muka samu labari yana zauna ne a cikin garin Funtuwa a Unguwar tsohuwar kasuwa.
Sai wani daga cikin hadiman kwamishinan ya zo ya gaya masa irin halin da yaron yake ciki na matsalar samun karaya a tsakiyar kashin bayansa, wanda sanadiyyar hakan wani asibiti ya tabbatar masu da cewa za a yi wa yaron aiki domin a gyara masa kashin amma sai iyayen sun kawo kudi naira miliyan 1,150,000 sannan za a iya yi masa aikin.
A wannan hoton za a iya ganin hadimin kwamishina mai suna Lawal Salimu da ya yi sanadiyyar biyan kudin domin ceton wannan yaro mai suna Mu’azu Lawal cediyar liyo a tsohuwar kasuwar Fintuwa cikin Jihar katsina
Cikin hukuncin Allah nan take kwamishina Hanza Sule Faskari ya ce a kaishi kuma a halin yanzu har an gama maganar yaron na can asibiti sai aiki kawai domin maganar kudi an rigaya an gama sai fatan Allah ya ba yaro lafiya da tsawancin kwana.
Zaku iya ganin hoton yaron a cikin wannan labarin.

About andiya

Check Also

Ramadan /Lenten 2023: Kaduna pastor  shares bags of grains to Muslim and Christian journalists .

Few days the after the massive distribution of foodstuffs to over 1000  less privileged Muslims …

Leave a Reply

Your email address will not be published.