Home / Ilimi / An Rufe Makarantar Nuhu Bamalli Da Ke Zariya

An Rufe Makarantar Nuhu Bamalli Da Ke Zariya

 Imrana Abdullahi

Sakamakon irin matsalar kai harin da yan bindiga suka yi makarantar Nuhu Bamalli da ke Zariya inda aka rasa rayuwa tare da kwashe wadansu dalibai ya sa hukumar makarantar ta sanar da Dakatar da harkokin ilimi na koyo da koyarwa  baki daya har sai illa masha Allahu.

A cikin wata takardar sanarwa a madadin mai rikon mukamin magatakardar makarantar, wadda ke dauke da sa hannun  jami’in yada labarai Mahmud Aliyu Kwarbai, ta sanar da cewa an Dakatar da harkokin karatu a makarantar sai illa masha Allahu.

Don haka dalibai ana umartarsu da su hanzarta ficewa daga makarantar nan take.

Sai dai hukumar makarantar ta sanar cewa ga daliban da za su yi jarabawar share fagen shiga jami’a IJMB da jami’ar Ahmadu Bello ke shirya wa su za su fara rubuta jarabawar a ranar Talata 15 ga watan Yuni 2021.

About andiya

Check Also

APC SOKOTO FLAGS OFF STATE-WIDE CAMPAIGN IN WAMAKKO LG, UNVEILS 8-POINT AGENDA

  The All Progressives Congress (APC), Sokoto State chapter on Wednesday flagged off its state-wide …

Leave a Reply

Your email address will not be published.