Home / Kasuwanci / An Bude Gidan Man A A Rano Na Millenium City Kaduna

An Bude Gidan Man A A Rano Na Millenium City Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi

An Bayyana kamfanin saye da sayar da albarkatun man fetur na A A Rano da cewa kamafani ne a koda yaushe yake kokarin kyautatawa al’umma baki daya.

 

 

Alhaji Ibrahim Abdullahi Attamra, daya daga cikin taraktocin kamfanin ya bayyana hakan a wajen taron bude gidan mai da kamfanin A A Rano Nigeria Limited ya samar a unguwar dan bushiya da ake kira Millenium City cikin garin Kaduna.

 

 

Inda ya bayyana cewa babbar manufar kamfanin A A Rano ita ce ci gaba da bunkasa tattalin arzikin Najeriya da kuma kyautatawa al’umma baki daya.

 

 

Attamra, ya ci gaba da bayanin cewa bisa wannan dalili ne suke kokarin fadakar da jama’a cewa duk inda wani ya ga wani lamarin da ke bukatar gyara dangane da irin ayyukan da suke gudanarwa a ko’ina da ayi magana saboda tamkar gidan man na kowa ne manufa ita ce yin gyara, saboda tsari ne na kyautatawa al’umma a koda yaushe”.

 

 

Ya ci gaba da cewa sun dauki ma’aikata a wannan katafaren gidan man da aka bude a yau,kuma wadanda aka dauka yan asalin Jihar Kaduna ne saboda bisa al’ada duk inda suka gina tare da bude gidan mai to, yan asalin Jihar ne ake dauka”, inji Abdullahi Attamra.

 

 

“Muna godiya ga daukacin Sarakuna iyayen kasa tun daga kan mai martaba Sarkin Zazzau, da dukkan Sarakuna baki daya da masu aikin jami’an tsaro da duk shugabannin jama’a da mabiyansu baki daya bisa irin bisa irin yadda suke bayar da cikakken hadin da goyon baya ga kamfanin A A Rano a koda yaushe.

 

 

A lokacin bude wannan gidan mai an rabawa mutane mai kyauta kamar yadda ya kasance al’adar kamfanin A A Rano duk inda aka bude gidan mai sai an rabawa jama’a mai kyauta.

 

 

Kuma “jama’a ko ba a bayar da mai kyauta ba su na zuwa duk inda gidan sayar da man A A Rano yake su sayi mai saboda litar gidan man mai kyau ce, saboda haka muke matukar godiya da irin karamci da ake yi mana a ko’ina a duk fadin kasa baki daya”, inji Ibrahim Abdullahi Attamra.

 

Muna godiya ga dukkan shugabannin wannan Jihar ta Kaduna godiya ta musamman ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I, da dukkan shugabannin wannan wuri domin hatta su DPO, masu jagorantar al’umma, kungiyar NURTW da sauran kungiyoyin da suke hudda da su, duk da su aka bude wannan babban gidan mai mai tarin albarka na kamfanin A A Rano da ke kasuwancin dukkan albarkatun mai da suka hada da Fetur da Gas da sauransu,.

About andiya

Check Also

Samar Da Tsaro Sai Kowa Ya Bayar Da Gudunmawarsa – Kaftin Joji

….A koma ga masu unguwanni, dagatai da hakimai Kaftin Muhammad Joji ya bayyana cewa lallai …

Leave a Reply

Your email address will not be published.