Home / Labarai / An Sace Dala Tiriliyon Talatin – Mahadi Shehu

An Sace Dala Tiriliyon Talatin – Mahadi Shehu

 

Mustapha Imrana Abdullahi
Dan Gwagwarmayar kwato wa jama’a yanci Dokta Mahadi Shehu ya bayyana binciken tonon sililin da yan jarida na duniya  suka yi a matsayin babban al’amarin da ba a yi tsammani ba, sakamakon gano satar kudin da aka yi da suka kai dala tiriliyan Talatin.

Ya ce wadannan yan jarida na duniya sun zabo kawunansu ne domin gudanar da binciken sililin da suka yi shi ne sakamakon irin karuwar da arzikin duniya yake yi domin an gano ma’adinai, kafafen sadarwa da suka taimakawa arzikin duniya bunkasa amma kuma yawan mutane na kara shiga cikin talauci cututtuka da yawa suna karuwa sai suke tambayar kawunansu shin wai ina arzikin nan ne da ake tunkaho da shi.
A kokarin aiwatar da wannan binciken akwai jarida ta yanar Gizo guda daya daga Najeriya ita kadai ce kawai aka saka acikin wannan binciken wato “premiumtimes” its kadai ce kawai ta shiga binciken kuma sun bincika takardun asusun ajiya na Banki, na kamfanoni da hannun jari guda miliyan sha daya da dubu dari Tara, na takardu kawai.
Suka kuma yi wa takardun nan sala sala inda suka gano cewa shugabannin kasa masu ci a yanzu guda 36 da wadanda suka ci da can fiye da Hamsin sun ajiye kudade da yan siyasa fiye da dubu uku, akwai yan Najeriya ciki har da tsohon shugaban kasa da Gwamnoni masu ci da wadanda suka wuce ya zuwa yanzu domin ba a kammala binciken ba tukuna da yan majalisa da Alkalai manya manya a hade baki daya an saci kudi an kai wata yar karamar kasa inda ba a haraji, ba tonon silili ba a fadin sunan mai kudin sai a yanzu da aka samo takardun aka gano hakan cewa an sace Dalar Amurka Tiriliyon Talatin.
“Duk kwamfutar da ka bugawa dala tiriliyan Talatin sau dari biyar da Tamanin ba za ta iya dauka ba sai kuma wanda zai iya lisaafi ya fadi nawa ne kudin a cikin lisaafin naira da aka sace tsakanin shugabannin, yan kasuwa, yan majalisa nada da na yanzu a cikin duniya wanda Najeriya na cikinsu suka yi wannan satar kudin.
“An kuma kai wannan kudin ne a cikin wata karamar kasar da gaba daya arzikin ta bai kai tiriliyan daya na dala ba sam sam ba su da arzikin tiriliyan daya amma aka kai masu wannan kudin na sata tiriliyan Talatin, to abin kunyar ma shi ne zaka ga mutum daga Najeriya ya saci kudin kuma kokari yake yi domin ya nesanta kansa da su duk da shi ya sace su”, inji Mahadi Shehu.
Ya kara da cewa shi yasa zaka ga Bature yazo Najeriya daga shi sai jaka kawai me yazo yi yazo ne tallar yadda zaka dauki kudin sata ka kai kasashen waje kawai, domin zai gaya maka ina sayar da sirri, ina ajiye sirri kuma ni mai sirri ne saboda haka ka ba ni saboda haka ka ba ni siirinka Sato ka ba ni kudi ba sunanka ba ainihin sa hannunka zan je kasa kaza zan bude maka kamfani ka ba ni sunayen daraktocin da kake so a kamfanin zan bude maka kamfanin ba za a Sanya sunanka ba, zan bude maka asusun ajiya na dala,euro da fam din Ingila zan kuma zuba maka hannun jari a kamfanonin duniya kudin na ciki naka ne sai dai dan kamashon da zaka rika ba ni.
“Amma inda Allah ya tona masu asiri shi ne sai a Sanya sunayen yayansu, ko matar da suke aure, to inda tonon asirin yake shi ne  zaka ga dan nan ko matar nan yan makaranta ne, da akwai wadanda ake gani masu kudi ne sun goge amma duk ashe kudin sata ne kuma da hakan ne aka Talauta Najeriya”, inji Mahadi.
Ya kuma bayar da wani misalin da cewa wata satar ma da wasu ke yi Mara amfani ce ga jama’a domin wanda ya saci kudi ya kai kasar Ingila su da ba su da komai na ma’adanin karkashin kasa domin ba Fetur,Kuza ko farar kass sai dai gidajen haya kawai da kuma haraji na rashin hankali, sai kuma yayan Najeriya da ake dauka akai kasar Ingila su yi karatu wanda duk dan Najeriy da aka kai Ingila ya yi karatu kudin makarantarsa sai ya biyawa dan kasar Ingila yaro biyar kudin makaranta a haka suke tsarinsu.
Saboda sai ka ga dan Najeriya ya biyawa yaronsa kudin makaranta Fan dubu Ashirin da biyar, to, a ciki sai an biyawa dan Ingila mutum biyar kudin makarantarsa,abincinsa da na wurin kwanansa a hannun dan Najeriya guda daya.
“Kana nufin irin wannan kasar zaka saci kudi ka kai mata ta dawo maka da su, misali ko ka kai kasashe irinsu Amurka,Swizerland su dawo maka da kudin da ka kai ajiya can babu ba zai yuwu ba sam, kuma shi ya sa ba zaka ji komai ba indai ya na da kudi a kasar ya fi dan kasar matsayi saboda an san da ya mutu shikenan ko magadansa ba abin da za su samu saboda ai ga shi nan an mutu da yawa amma an kasa samo kudin da aka kai ajiyar”, inji Dokta Mahadi Shehu.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.