Home / News / An Samu Gawar Shugaban APC Na Jihar Nasarawa Da Aka Sace

An Samu Gawar Shugaban APC Na Jihar Nasarawa Da Aka Sace

An Samu Gawar Shugaban APC Na Jihar Nasarawa Da Aka Sace

Imrana Abdullahi

 

Wadansu mutanen da har yanzu ba a san ko su waye ba da suka sace shugaban jam’iyyar APC na Jihar Nasarawa Mista Philip Schekwo a Daren Jiya, a halin yanzu an tsinci Gawarsa

Shi dai wanda aka sacen ya taba zama kwamishinan ma’aikatar ciniki da masana’antu na Jihar Nasarawa a lokacin Gwamna Tanko Al’Makura.

 

A halin yanzu dai bayanai daga Jihar ta Nasarawa na cewa Gwamna Abdullahi Sule da mataimakinsa tare da tsohon Gwamna Tanko Al’makura sun ziyarci wurin da aka ga Gawar mamacin.

 

An dai ga Gawar tasa ne a yan mitoci kadai daga gidansa, a yan mintocin da suka wuce.

 

Shi dai Schekwo dan asalin karamar hukumar Toto ne ta Jihar Nasarawa.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.