Home / Labarai / AN Sace Shugaban Kungiyar Kiristoci Ta Kasa Reshen Nasarawa

AN Sace Shugaban Kungiyar Kiristoci Ta Kasa Reshen Nasarawa

Imrana Abdullahi
Tsohon sakataren kungiyar  Yohanna Samari, ya tabbatarwa da kafar yada labarai ta Resiyon Gwamnatin tarayya ( FRCN) cewa wadansu da ba a san ko su waye ba sun sace shugaban kungiyar Kiristoci reshen Jihar Nasarawa Bishop Joseph Masin da sula shigo cikin gidansa a Bukan Sidi a garin lafiya Jihar Nasarwa.
 Yohanna Samari ya ce mutanen sun zo ne da misalin karfe 11 na daren ranar Laraba zuwa karfe 12 na talatainin Dare.
Kwamishinan yan sanda na Jihar Mista Bola Longe ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya kara da cewa wadanda suka sace shugaban kungiyar kiristocin su dauke shi ne a kan Baburan hawa.
 Bola Longe ya kuma tabbatarwa da manema labarai cewa jami’an yan sanda na iya bakin kokarinsu domin tabbatar da kubutar da shugaban kungiyar na CAN.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.