Home / Lafiya / Har Yau Gwamnati Bata Zauna Da Mu Ba – Sakatariyar Kwadago

Har Yau Gwamnati Bata Zauna Da Mu Ba – Sakatariyar Kwadago

Har Yau Gwamnati Bata Zauna Da Mu Ba – Sakatariyar Kwadago

Mustapha Imrana Abdullahi
Sakatariyar Kungiyar Kwadago reshen Jihar Kaduna kuma sakatariyar kungiyar ma’aikatan da ke aiki a asibiti Uwargida Christy John Bawa, ta bayyana cewa har ya zuwa yanzu Gwamnatin Jihar Kaduna bata zauna da yayan kungiyar kwadagon Jihar ba.
Uwargida Christy, ta bayyana hakan ne lokacin da take gabatar da wani shirin tattaunawa a kafar Talbijin ta Jihar Kaduna, a cikin shirin safe na Kalachi.
Uwargida Christy, ta ci gaba da cewa kamar yadda ba a tattauna da su a matsayin ma’aikatan Jihar Kaduna lokacin da za a cire masu kashi 25 a cikin albashinsu ba, haka nan har yanzu ba a kira su domin tattaunawa da su ba bayan fara yin yajin aikin gargadi da suka fara na tsawon sati daya.
” Muna son a mayar mana da kashi 25 da aka cire a cikin albashinmu na ma’aikata, saboda haka muke yon kira ga Gwamnati da lallai lallai ta mayar mana da kashi 50 na albashinmu da aka cire mana, kuma a wani wata mai zuwa kada a ci gaba da cire mana albashi”.
” Mutane da da suka hada da ma’aikata suna cikin wahala kuma daman albashin da ake samu ba Isa yake yi ba kuma ga nauyin da ke wuyan dukkan wanda ke daukar Albashi don haka Gwamnati ta duba wannan”.
Sai ta bayyana cikakkiyar godiyarta ga ma aikata bisa irin yadda suke bayar da cikakken hadin kai da goyon baya a duk lokacin da kungiyar kwadago ta kira su domin daukar matakin da zai tabbatar wa da yayan kungiya wata nasarar da ake bukatar a samu.
Ta ci gaba da cewa ta yaya ma’aikatan asibiti za su ta fi yajin aiki amma Gwamnati bata kira su ta zauna da su ba domin samo bakin zaren, ya kamata fa a rika duba ainihin bukatun jama’ar da suka zabi Gwamnati musamman ta fuskar kiwon lafiya
” Asibitoci da dukkan cibiyoyin kula da lafiyar jama’a sun kasance a kulle, to ina talakawan kass za su sa kansu musamman a cikin wannan lokaci na yaki da cutar Korona”.
Ta kuma mika cikakkiyar godiyarta ga daukacin manema labarai da suke kokarin yada Labaran abin da kungiyar kwadago ke ciki, da kuma tuntubarsu domin jin nasu bangaren a halin da ake ciki.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.