Home / Labarai / An Saki Dalibai Mata 279 Da Aka Kama A Jihar Zamfara

An Saki Dalibai Mata 279 Da Aka Kama A Jihar Zamfara

An Saki Dalibai Mata 279 Da Aka Kama A Jihar Zamfara
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Muhammadu Bello Matawallen Maradun ya bayyana samun nasarar kubutar da dalibai mata da yan bindiga suka kwashe daga makarantarsu a garin Jangebe.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawar da ya yi da kafar yada labarai ta bbc hausa, inda ya ce hakika an samu nasarar sakin wadannan dalibai su 279 kuma dukkansu na cikin koshin lafiya domin babu abin da ya samesu.
Ga hoton daliban da aka kama nan
Gwamnan ya tabbatar da cewa ba a bayar da kudin fansa ba kafin sakin wadannan dalibai Mata.
“Mun yi amfani da wadanda suka amince da yin sulhu ne da suka kai sama da mutum Talatin (30) su suka rika yin magana da wadanda suka dauki yaran kuma cikin ikon Allah an samu nasarar sakinsu.
Sai dai Gwamnan ya yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta samar da wadatattun jami’an tsaron da za su samar da tsaro a dukkan makarantu kasancewar a yanzu sun yi kadan, ” ko a can Jangebe da aka dauki daliban nan kusa da jami’an tsaro ne amma lamarin ya faru don haka akwai bukatar a kara yawan jami’an tsaro”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.