Daga Imrana Abdullahi
Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar NDC Alhaji Ibrahim Husaini Abdulkarim da ake yi wa lakabi da Malam Zitar, ya bayyana cewa da yardar Allah zai tabbatar da samun hadin kai da kaunar juna a Jihar Kaduna baki daya idan ya zama Gwamna.
Ibrahim Husaini wanda ya tsaya takarar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar NDC ya bayyana hakan ne a lokacin da ya tattauna da manema labarai a wajen babban taron jam’iyyar karo na farko a Kaduna.
Ibrahim Husaini Abdulkarim da ake yi wa lakabi da Malam Zitar, ya ce hakika lokaci ya yi da wadanda suka bata kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin al’ummar Jihar Kaduna tun asali da aka sani da lallai irin wadancan mutane su ja da baya domin matasa su gyara al’amuran da ke tsakanin jama’a kowa ya ci moriyar Arziki da dukkan ni’imar da Allah ya yi wa Jihar Kaduna.
Malam Zitar, ya bayyana gamsuwarsa da irin yadda jam’iyyar NDC ke kara samun karɓuwa a dukkan mazabun jihar wanda ko a wurin babban taron da jam’iyyar ta gudanar a dakin taro na Otal din Asaa da ke Kaduna, kowa ya shaida irin yadda ya’yan jam’iyyar suka zo daga matakin Mazabu, Kananan hukumomi da mataki na Jiha wanda hakan abin a ya ba ne kwarai tare da farin ciki.

“Sannan ga shugabannin jam’iyyar a kowane irin mataki tun daga Mazabu, Kananan hukumomi da Jiha, duk tare da yan takarar majalisar Jiha da na Majalisar tarayya duk sun zo wurin taron ana kuma yi tare ba wani bambanci ballantana a samu wata rigima Sam babu ko daya.
Kuma ai wannan jam’iyyar ta NDC jam’iyya ce da ta fi kowace jam’iyya saurin karɓuwa da ci gaba a halin yanzu, saboda a cikin watanni Uku babu wata jam’iyyar da ake maganarsa a Najeriya kamar NDC ana maganar NDC ne saboda irin jajirtattun mutanen da muke da su a cikin jam’iyyar irin su Kwankwaso da Peter Obi da kowa ya san manufarsa da abin da yake son ya kawo a Najeriya. Sannan kuma mataimakin sa da za su tsaya takara tare wato Sanata Kwankwaso da kowa ya san shi a arewa mutum ne mai son ya kawo taimako da agaji ga ya’yan talakawa da wadanda ba kowa ba a kasa don haka ne muke ganin wannan tafiya ce ta matasa da ikon Allah zamu kai ga ga ci.
Da yake mayar da martani ga masu cewa wai ko jam’iyyar ta karbo Kwangila ne daga wani wuri kuwa, Sai Malam Zitar, ya kada baki ya gaya wa yan jarida cewa da akwai a ƙalla watanni Takwas a nan gaba don haka idan an yi zabe aka kifar da masu cewa an karbo Kwangila za a ga Ni Ko ita ce ko ba ita ba kwangilar ba ce aka ba su ba.

“Domin shi irin wannan abu mutane ne da aka biya su suke yin irin wannan yarfen na siyasa a rika kiran jam’iyyar ta Inyamirai ko wani addinancin da ake sanya wa a harkar duk wanda yake kawo kabilanci da addinanci a cikin siyasa lallai ba shi da wani abu da zai yi bayani ne a kai ba abin da zai nuna wa jama’a kuma sai ya dauki wani abu da mutanen ke amfani da shi ya kawar da hankalinsu daga abin da ya dace su sani ko su aikata na ci gabansu.
“Ya da ce dai wannan lokacin na yanar gizo da ake ciki mutum ya tambayi matambayi baya ba ta na yanar Gizo ko wane ne ya sa aka yi wa yan arewa Katin shaidar zama a jihar sa zai bayar zai nuna maka wanda ya sa aka yi da ranar da aka yi ga kuma abin da aka yi kada mutane su zauna haka kawai sai dai su saurari dandalin fezbuk da tiktok, domin yanar Gizon da aka samawa jama’a da ke a hannuwansu shi ne damar da suke da ita.

Saboda da haka ne,” muke gaya wa jama’a cewa su kula da duk wanda ba shi da abin da zai gaya maka ko ya yi maka na ci gaba sai dai kawai ya rika gaya maka Arewa Arewa arewa kawai, sai ka tambaye shi shugabannin Arewa da suka yi me suka yi wa Arewa da suka samu shugabancin Najeriya? Kada ka bari ya yi maka amfani da kabilanci ko addini, kawai abin da kake nema adalin shugaba da zai taimaka wa kasa ta ci gaba kuma ya tabbatar da an samu Asibitoci masu kyau, wutar lantarki, ruwan sha da tsaro mutane sun koma Gona da dai sauransu, mu a nan a garin Kaduna babban abin da muke kokarin yi da jama’ar da nake tare da su shi ne rayuwa ta zama abin da ya fi komai amfani ya zama mutuwar mutum daya dan Kaduna ita ce larurar da ya fi komai zafi a Kaduna don haka nake son muke son Kaduna ta koma irin yadda take a can baya Kirista da Musulmi suna yin zamantakewar al’amuran tare ba tare da kiyayya ko kwamar juna ba kamar yadda lamarin yake a can shekarun baya kowa ya san dadin da Kaduna take da shi.

Amma daga shekarar 1999 zuwa yanzu suka sa aka yi ta fadace fadace ana raba kan jama’a domin su ci gaba da yin mulki, amma mu idan Allah ya sa mun karba zamu yi kokarin mayar da kan mu yadda muke a can baya kamar da can ta yadda ya’yan mu za su taso cikin amana cikin mutunci domin idan sauran matasan duniya baki daya muka bar masu irin wannan rayuwa ta bakin ciki da hassada da rayuwar rabe rabe lallai ba abin da muke bukata ba ne saboda haka ya dace mu tayar da su cikin yanayi na Soyayya da taimakon juna su hadu su yi wasan ƙwallo tare su hadu su ta fi makaranta tare har ma su kirkiri wani abu sabo da can baya babu shi wannan ne abin da Allah ya ba mu ba wai rarrabe rarrabe kawuna ba

Ibrahim Husaini ya kuma yi kira ga matasa da su shiga cikin harkokin siyasa a dama da su ta yadda za su magance matsalolin da matasa Maza da Mata suke fuskanta sakamakon son Rai na wadansu mutane.
THESHIELD Garkuwa