Home / Big News / Ya’yan Jam’iyyar APC Sun Yi Zanga Zanga A Kaduna

Ya’yan Jam’iyyar APC Sun Yi Zanga Zanga A Kaduna

Wadansu ya’yan jam’iyyar APC daga daukacin kananan hukumomin Jahar Kaduna 23 sun taru a yau 19 ga watan Mayu,2026 a cibiyar yan jarida ta kasa reshen Jihar Kaduna inda suka yi gagarumar Zanga Zanga lumana tare da yin jerin Gwano zuwa ofishin jam’iyyar na Jiha domin bayyana fushinsu da abin da suka ce an yi kama karya.
Ya’yan jam’iyyar karkashin jagorancin yan takarar majalisar dattawa da yan takarar majalisar wakilai sun taru duk tare da dimbin magoya bayan su a  cibiyar yan jaridu ta kasa reshen Jihar Kaduna inda suka shaida masu cewa ba a yi zaben fitar da yan takara ba Sam a mazabun jihar kamar yadda dokar jam’iyya ta tanadar, wanda kuma yin hakan ci baya ne ga APC tare da ya’yan ta baki daya.
Yan takarar sun yi tabbatar wa da manema labarai cewa su da kansu ba su ga Malaman zabe ba kuma ba su ga kayan zabe ba ba a gaya masu wuri da lokacin da za a gudanar da zaben ba duk da cewa zabe ne na cikin gidan jam’iyyar APC a Jihar Kaduna.
Saboda haka kamar yadda suka shaidawa manema labarai cewa ba su amince ba kuma suna son ayi masu adalci, ayi zabe kamar yadda dokar jam’iyya ta tanadar.
Hakazalika ya’yan jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna sun yi tattaki zuwa ofishin jam’iyyar na Jihar Kaduna inda a can ma suka bayyana korafinsu cewa suna bukatar ayi masu adalci ayi zabe kamar yadda dokar jam’iyyar ta tanadar ta yadda za a samu nasarar lashe zabe a kowane irin mataki a jiha da kasa baki daya.
“Muna goyon bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kuma lallai muna yi masa aiki domin ya samu nasara, amma ya dace ya tambayi Gwamnan Kaduna Sanata Uba Sani me yasa yake yi wa ya’yan jam’iyya irin abin da ya aiwatar a kansu da sunan zaben fitar da yan takara a matakin Majalisar Wakilai da matakin Majalisar daitawa”, inji ya’yan APC na Jihar Kaduna.
Ya’yan jam’iyyar APC’n Maza da Mata ne suka taru domin yin wannan Zanga Zanga lumana daga Mazabu da akwatunan zabe da ke xaukacin kananan hukumomin baki daya.

About andiya

Check Also

Shettima Yerima Ya Janye Takararsa

Shettima Yerima Ya Janye Takararsa Daga Imrana Abdullahi A cikin wani yanayi mai ban al’ajabi …

Leave a Reply

Your email address will not be published.