Home / Big News / An Yaba Tare Da Yin Jinjina Ga Shetima Yerima

An Yaba Tare Da Yin Jinjina Ga Shetima Yerima

 

…Muna godiya ga Shetima Yerima
Daga Imrana Abdullahi
Sakamakon irin ayyukan inganta rayuwar al’umma musamman ma Talakawan da ke cikin Halin kunchi da Neman abin da za su ci a yau da kullum ya sa al’ummar Jihar Kaduna da Arewacin Najeriya ke bayyana gamsuwarsu da jinjinawa Babban Kwamared Mai fafutukar kwato Yancin Jama’a Shetima Usman Yerima, da ke Neman Sanatan yankin Kaduna ta tsakiya.
Kamar dai yadda jama’ar ke cewa tuni suka Lura da cewa Kwamared Shetima Usman Yerima ya cancanci ya Jagoranci al’ummar yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta kasa.
A Binciken da muka gudanar mun gano cewa Shetima Usman Yerima a kullum babu abin da ya Sanya a gaba sai kokarin taimakawa Jama’a musamman masu karamin karfi da suka hada da marayu da masu bukata ta musamman.
Mun kuma gano irin yadda Kwamared Shetima Usman Yerima ke bayar da gudunmawa wajen ci gaban masallatai da suka hada har da na masallatan juma’a.
Zaka ga Jama’a talakawan na kasa suna ta kukan farin cikin abin da Shetima Usman Yerima ya yi masu na alkairi Wanda kamar yadda suke Fadi ba su yi zato ba, ba kuma tsammani sai kawai suka ga ya biya masu bukatunsu ba tare da wata tantama ba.
Jama’a da dama suna ta cewa daman sun dade suna Jin suna da irin fafutukar da Shetima Yerima ke yi a kafafen yada labarai da suka hada da Talbijin, Rediyo da Jaridu, don haka abin da ya yi masu na taimako hakika ya Sanya su a cikin farin Ciki.
Don haka suke ta addu’a dare da Rana a Kan Allah ya ba wannan bawan Allah nasarar Zama Dan majalisar dattawa domin ya je Abuja ya ci gaba da nemawa Jama’a Yancin su kamar yadda ya Saba.

About andiya

Check Also

Dangote headlines 2026 Gateway Trade Fair as Gov Abiodun hails Group for boosting Ogun’s Industrial Competitiveness

Ogun State Government has lauded the roles being played by the Pan-Africa conglomerate, Dangote Industries …

Leave a Reply

Your email address will not be published.