Home / Labarai / An Yi Addi’oin Musamman  Domin Samun Zaman Lafiya A Katsina

An Yi Addi’oin Musamman  Domin Samun Zaman Lafiya A Katsina

 A ranar Litinin din  da ta gabata ne 1 ga watan Augusta shekara  ta 2022   a ka gudanar da addi’oi na musamman a kananan hukumomin Funtuwa da Dandume da Bakori da Danja da karamar hukumar Sabuwa da ke Jihar katsina domin samun zaman lafiya da walwalar jama’a
Dalilin wannan taron addu’o’in ya biyo bayan irin yadda sha’anin tsaro ya tabarbare a yankin da  yadda ‘yan ta’adda ke cin karensu ba babbaka a yankin dama kuma sauran sassan jihar.
Addu’ar ta sami halartar manyan malaman izala da darika na dukkan kananan hukumomin yankin addu’ar wadda ake kira da (yaumal  shukur) wadda ake gabatarwa duk shekara angudanar da karatun Alkur’ani maigirma da sauran addi’oi tunda misalin karfe 10 ma safiyar ranar aka fara gudanar da addioin a dukkan dakunan taro na kananan hukumomin.
                                      Dukkanshuwagabannin kananan hukumomin tare da hakimansu da kansilolin kananan hukumomin suka halarci taron addi’oin
A lokacin da suke nuna jindadinsu da kuma godiya ta musamman ga maigirma Gwamnan jihar Alhaji Aminu Bello Masari shuwagabannin kananan hukumomin na Funtuwa Malam Lawal Sani Matazu Wanda sakataren karamar hukumar Malam Salihu Danladi ya wakilta tare da hakimin Funtuwa Sarkin Maskan katsina Alhaji Sambo idris Sambo da sauran manyan jami’an karamar hukumar da shugaban karamar hukumar Bakori Alhaji Ali maicitta da hakimin Bakori Alhaji Idris sule idris dana Danja Alhaji Rabo Tambaya Danja da hakimin Danja sarkin kudu Alhaji Bature da shugaban karamar hukumar Dandume Alhaji Ya’u nowa da takwaranshi na karamar hukumar Sabuwa Alhaji Faruku Hayatu da kogon katsina hakimin sabuwa injiniya Bello Ibrahim sun yabawa dukkan malaman yankin da sauran jama’ar yankin ganin yadda suka tashi tsaye wajen gudanar da irin wadannan addi’oin domin samun zaman lafiya kuma suma zasu cigaba da gudanar da irin wadannan addioin duk wata a dukkan kananan hukumomin nasu

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.