Home / Lafiya / An Yi Kira Ga Buhari Ya Duba Halin Da Jama’a Suke Ciki – Gambo Tuge

An Yi Kira Ga Buhari Ya Duba Halin Da Jama’a Suke Ciki – Gambo Tuge

Imrana Abdullahi

Shugaban Kungiyar Katsinawa da Daurawa na kaduna kuma sakataren kudi na kungiyar Direbobin tanki ta kasa kwamared Gambo Ibrahim Tuge, ya kara ankarar da jama’a kan su rungumi kaddara game da cutar Korona Bairus da ke yi wa duniya barazana.

Gambo Ibrahim Tuge ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a kaduna.

Gambo Tuge ya ci gaba da cewa ya zama wajibi ga jama’a su amince da cewa cutar gaskiya ce don haka ya rungumi batun rigakafi da duniya ta runguma.

Tuge ya kara jaddada cewa dole mutanen Nijeriya baki daya suyi hakuri su kuma rungumi kaddara domin Allah ke kawo kaddara kuma ya kawo maganin ta don haka hakuri yana da muhimmanci kwarai.

Kwamared Gambo Tuge ya kuma yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya duba sosai domin waiwaya mutanen da suka zabe shi wato Talakawa domin suna cikin wani hali da suke neman taimako matuka.

“Wani sai ya fita sannan zai samu abin da zai ci saboda haka idan abin ya yi tsanani sai an duba Talakawa sosai, don haka ya Sani cewa mutane suna cikin wani hali mai wahalar gaske, domin jama’a na tasowa daga wadansu wurare suzo su ce mana ba su ci abinci ba don haka ana cikin wani hali, dole mai imani ya tausaya ya duba halin da jama’a ke ciki”.

” Gwamnatin tarayya ta duba halin da manoma ke ciki na rashin darajar amfanin Gona, da kuma duba irin yadda ake yi wa manoma wulakanci, domin a can baya ana sace shanu ne amma a yanzu mutanen baki daya ake sace wa ana karbar kudin fansa domin kawai su manoma ne don haka muke yin kira ga Gwamnati.

Don haka shugaban kasa da sauran Gwamnoni su duba halin da ake ciki a taimakawa manoma saboda mutum na son yaje Gona ko ya yi Noma amma gaban mutum na faduwa don haka a duba sosai halin da jama’a ke ciki, saboda ba su san komai ba sai Noman shi suka iya kuma suke yi, saboda haka su Sani kamar Gobe ne za a zo ace ana neman kuri’ar jama’a.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.