Home / KUNGIYOYI / An Yi Kira Ga Gwamnati Ta Sauke Nauyin Da Ke Kanta

An Yi Kira Ga Gwamnati Ta Sauke Nauyin Da Ke Kanta

An Yi Kira Ga Gwamnati Ta Sauke Nauyin Da Ke Kanta

Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban kungiyar Gan Allah Fulani Develipment Association Of Nigeria ( GAFDAN) Alhaji Sale Bayeri, Bauran Wase ya yi kira Gwamnatin tarayyar Nijeriya da daukacin Jihohi baki daya da su sauke nauyin da ke wuyansu game da hakkin Fulani musamman makiyaya da ake cin zarafinsu ba gaira ba dalili.
Alhaji Sale Bayeri, Bauran Wase ya bayyana hakan ne a wajen babban taron kaddamar da yayan kungiyar ta kasa reshen karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
Bauran Wase ya ci gaba da cewa hakika daukar matakin sauke nauyin da ya rataya a wuyan Gwamnatin ya zama wajibi saboda dukkan Fulani na da yanci da damar rayuwa kamar kowane mutum a fadin kasa baki daya.
Bauran Wase ya kuma yi kira ga yayan kungiyar Gan Allah a ko’ina suke a fadin kasa da Afrika baki daya su tashi wajen neman ilimi kasancewa sai da shi ne ake samun biyan bukatu da kuma ci gaban da kowa ke bukata.
Ya shaidawa yayan kungiyar a wajen taron da aka yi a unguwar Dan bushiya cewa ilimi ne zai yi jagora wajen ciyar da kowa gaba don haka tashi tsaye wajen nemansa ya zama wajibi domin hakan zai bayar da damar a tsira da mutunci.
“Ina da dan cikina da na haifa, da a yanzu keda shaidar kammala karatun digiri na biyu a shekaru 25 sai kuma mai karatun Likita ban da batun Cutar Korona da yanzu ta kammala a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, saboda haka da na samu gata kamarsu da a yanzu wani Farfesa ne a fannin Boko amma duk da haka Alhamdulillah”.
Sale Bayeri ya kuma fayyace cewa ban da kokari irin na al’ummar Fulani wajen samar da Nama da Nonon Sha, da ake amfani da shi  da yanzu asusun ajiyar Nijeriya na kasashen waje tuni ya rigaya ya kare
Ya kuma yi kira ga yayan kungiyar a ko’ina suke da su rika kiyaye doka tare da girmama hukuma domin hakan zai bayar da damar samun ci gaba sosai.
” A kuma yi tarbiyyar, ladabi da biyayya tare da rike gaskiya a kowace mu’amala tsakanin al’umma”.
Ya yi bayanin cewa sakamakon irin ayyukan da kungiyar Gan Allah take gudanarwa yanzu makiyaya na yin kiwon Dabbobinsu a kasar Taraba baki daya, kuma dukkan wuraren da yakamata a tashi tsaye a nema masu Hakkinsu ana kokarin yin hakan ba tare da gajiyawa ba.

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.