Home / Labarai / AN YI KIRA GA MANIYYATAN JIHAR BAUCI SU KARA HAKURI

AN YI KIRA GA MANIYYATAN JIHAR BAUCI SU KARA HAKURI

….A Shirye Muke Mu Mayarwa Masu Bukata Kudinsu
Hukumar jindadin alhazai ta Jihar Bauchi ta kira yi Maniyyata aikin hajjin Bana da su kara hakuri, su kuma zauna a gidajensu har zuwa lokacin da aka bada sanarwar lika jadawalin jirginsu.
Babban Sakataren Hukumar, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris, shi ya yi Kiran a yayin da yake jawabi wa manima labarai a sansanin alhazai da ke Bauchi kan halin da ake ciki na ci gaba da jigilar Alhazan jihar.
Ya nuna rashin jindadinsa kan yadda mutane ke cin-cirindo a shalkwatar hukumar da kuma sansanin Alhazai gabannin saukar  Bizar su na tafiya kasa mai sarki.
Imam Abdurrahman ya ce saukar Bizar maniyaci ba hurumi ne na Hukumar Alhazai ba, ya jaddadda bukatar davke akwai na maniyyatan da su kara hakuri, inda ya ce hukumarsa a shirye take da ta fara maida kudaden aikin hajji ga maniyyatan da ke bukatar kudinsu daga ranar Litinin 5/06/2023
Ciki farin cikin, Imam Abdurrahman ya ce Alhazan jihar Bauchi jirgi na Daya (1), Dana Biyu (2), suna garin Madina cikin koshin lafiya, kana na uku (3), na filin jirgin sama don shirye shiryen tashin su zuwa kasa mai sarki, harwa yau akwai jirgi har hudu (4), da zasu biyo baya da yaddar Allah.
Ya kuma gargadi mutane da su dai na yada jita-jita kan hidimar aikin hajji, inda ya kara kira ga mutane da su bar hukumar tayi aikinta cikin lumana ba tare da tsangwa ba.
Bugu da kari da Imam Abdurrahman ya jaddadda kudirin gwamnatin jihar Bauchi na hidimawa bakin Allah wato Alhazai.
Daga Jihar Bauchi Jamilu Barau

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.