Home / Uncategorized / An Yi Kira Ga Shugabanni Su Yi Koyi Da Hajiya Naja’atu – Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun

An Yi Kira Ga Shugabanni Su Yi Koyi Da Hajiya Naja’atu – Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun

Daga Imrana Abdullahi

An yi kira ga daukacin shugabanni da dukkan Jagororin al’umma da su yi ko yi da Hajiya Dokta Naja’atu Muhammad domin a samawa Arewa da kasa baki daya mafita.

Shaikh Yusuf Sambo Rugachikun ne ya yi wannan kiran a lokacin da ta kai masa ziyarar gaisuwar ta’aziyyar rasuwar Dansa.

Shaikh Yusuf Sambo ya ce hakika idan da Malamai, Yan Siyasa da Sarakuna da dai dukkan sauran shugabannin jama’a za su jajirce kamar yadda Hajiya kike jajircewa lallai da an samu ci gaba a Arewa da kasa baki daya.

Shaikh Yusuf Sambo ya ce Ko lokacin da Farfesa Sani Rijiyar Lemo ya kawo masa ziyara kamar irin hakan inda ya shaida Mani cewa muna ta cewa harkokin siyasa sun lalace haka nan ne ma harkar malantar ita ma ta lalace, inji Yusuf Sambo kamar yadda Farfesa Sani rijiyar Lemo ya shaida masa.

“Yadda muke yin maganar siyasa ta lalace, haka ita ma Malantar ta lalace”
“Fatan my shi ne duk irin kwaranniyar da ake yi mu dawo kan sirdi mu gyara, my dubi irin abubuwan da su Sardauna suka yi kamar makarantar da koyon tukin Jirgin sama ta Zariya,asibitin koyarwa na ABU da ke Shika Zariya ga daliban da suka yaye, jami’ar Ahmadu Bello Zariya,Makarantar soron sojoji ta Zariya, makarantar kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna polytechnic da kwalejin horon Yan Sanda ta police college da Gidan rediyon tarayya na Kaduna da kuma Bankin arewa da aka kashe karfi da yaji aka mayar da shi Unity wanda a yanzu ma babu shi sam

Ga kuma wurare irin su Kayinji Dam da wadansu kamfanoni a Kano Sakkwato da wadansu wurare da yanzu aka kasa rike su balantana a inganta su ba ma a yi wadanda suka fi su ba, wanda a kullum abin da kike yin magana kenan na a dawo a hada kai sai wannan ya yi nan wancan ya yi can kuma nassin Alkur’ani ya ce kada ku yi jayayya domin karginku zai ta fi da duk karfin iyawarku, mulkinku da iyawarku duk za su watse indai ba ku da hadin kai da yawa da basirar ku duk za su ta fi.

Don haka sai ya yi kira ga Hajiya Naja’atu da daure ta ci gaba duk kalubalen da za ta hadu da shi ba komai saboda jahadi ne kuma Allah zai baki ladan abin da kike yi Allah kuma ba zai durkusar da ke ba, yadda kike bin duk wani babban mutum a Arewa kina gaya masa gaskiya ki ci gaba da hakan.

“Ina yi maki addu’ar Allah ya saka maki da alkairi ya kuma kara wa rayuwa albarka, mun gode sosai”.

An kuma yi wa Hajiya Naja’atu addu’a ta musamman domin samun yardar ubangiji, kariya da nasara a koda yaushe.

About andiya

Check Also

Aliko Dangote Hails IBB: ‘You’re the Architect of Private Sector in Nigeria’ 

… Donates N8bn to Presidential Library, Pledges N2bn Annually Until Completion The President and Chief …

Leave a Reply

Your email address will not be published.