Home / Labarai / An Yi Walimar Taya Soja Abdurrahman Abdullahi Shinkafi Murnar Zama 2nd Lieutenant A Kaduna

An Yi Walimar Taya Soja Abdurrahman Abdullahi Shinkafi Murnar Zama 2nd Lieutenant A Kaduna

Daga Imrana Andullahi

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Mahmuda Aliyu Shinkafi, yi wa Allah godiya ya yi da Abdurrahman marigayi Farfesa Abdullahi Muhamamd Shinkafi ya samu ya kammala kwas mai wahala daga makarantar horon Sojoji ta NDA Kaduna abin da ya bayyana da cewa hakan babbar alamace da ke nunin cewa yaron cikin ikon Allah zai kai duk inda ake kaiwa a rayuwar aikin Soja a duniya.

“Muna saran da ikon Allah shi da dan uwansa Abdulkadir Rikiji Rikiji su kai karshen mukamin soja da ake kaiwa na Janaral su zama manyan sojojin Najeriya da ikon Allah. Mahmuda Aliyu Shinkafi ya kuma yi addu’ar Allah ya gafartawa marigayi Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi da fatan mutuwa Hutu ce.

Da yake gabatar da nasa jawabin a wajen taron babban Alkalin babbar kotun Jihar Zamfara Mai shari’a Bello Muhammad Shinkafi, cewa ya yi a taro irin wannan akwai abin yin murna da kuma bakin ciki, abin farin ciki shi ne muna murnar namu ya kammala karatun makarantar horas da jami’an Sojoji kuma abin bakin cikin shi ne kasancewar babu Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi a raye ya zama marigayi da ya riga mu gidan gaskiya Alkah ya gafarta masa.

Daga Dama Janar Galadanci ne da ya halarci taron suke tattaunawa da Sanusi G Rikiji

Shawara ta ga Abdurrahman Abdullahi Shinkafi da ya kammala karatun Soja shi ne “Ka zama mai gaskiya ka zamo kamar mahaifinka da kuma zamo mai biyayya kwarai a koda yaushe. Ka duba irin manyan mutanen da suka taru a nan wurin duk da mahaifinka ba shi da rai, amma duk da hakan sun hallara a wannan taron tayaka murna ga sunan kama tsofaffin Gwamnoni, mataimakan Gwamnoni, Janar Janar na soja da suka yi ritaya da masu ayin aiki a halin yanzu ga kuma Farfesoshi na jami’a har da wanda ya taba yin shugaban jami’a duk a cikinsu saboda haka lallai abin farin ciki ne da murna kwarai don haka ka zamo mai gaskiya kamar mahaifinka ka zamo mai biyayya hakan zai sa ka ci duk wata nasarar da ake bukata a rayuwa, muna kuma fatan a nan gaba wata rana zamu taru mu yi murnar ka zama Janaral a rundunar Sojan Najeriya.

Da yake gabatar da nasa jawabin Farfesa Riskuwa Arabo Shehu fadakarwa ya yi ga jama’a cewa hakika wannan rayuwa mai karewa ce don haka kowa ya rika duba tare da aiwatar da duk wani al’amari bisa lura da abin da ya dace.

Farfesa Arabo ya ce “duk abin da muke yi mu ci gaba da tuna cewa zamu mutu a wata rana don haka sai mu kyautata zamantakewa a kan dukkan abin da Allah ya hukunta mu yi kuma a kan haka ne nake cewa Allah ya karfafa zumunci wadannan yaran kuma da a yanzu suke tasowa Allah ya albarkace su Allah ya yi masu jagora da kariya da kuma kasar ta amfana da tarbiyya da ilimin da aka ba su”, Farfesa Riskuwa Arabo Shehu ya jaddada a wajen taron.

Da yake gabatar da wani Dogon jawabin da ya yi a Wajen taron Honarabul Sanusi Garba Rikiji, wanda shi ne ya dauki nauyin taron baki daya da aka yi a otal 17 da ke cikin garin Kaduna.

Wannan shi ne 2nd Lieutenant Andurrahman Abdullahi Shinkafi

Sanusi Garba Rikiji, cewa ya yi babban dalilin shirya wannan taron shi ne domin bikin taya Abdrrahman Abdullahi Shinkafi murnar kammala karatun horas da jami’an Sojoji inda ya fita da matsayin 2nd Lieutent a matsayin jami’in sojan kasa SSI kuma domin a karfafa zumunci da ke akwai tsakaninsu tun da dadewa da Mahaifin yaron marigayi Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi wanda akwai daddiyar alaka ta zumunci da dadewa.

Wanda hakan ya sa ya kira ainihin dansa da ya haifa na cikinsa da ya kammala nasa karatun zama sojan a shekarar da ta gabata da kuma wanda ake yin taron domin sa wato Abdurrahman Abdullahi Shinkafi, ya tsaya a tsakiyarsu tare da tambayarsu cewa su yi alkawari a gaban mahalarta wannan taron cewa za su ci gaba da rikon zumunci da ke tsakanin iyalan biyu wato na Sanusi Garba Rikiji da kuma na marigayi Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi kuma nan take yaran biyu duk suka dauki wannan alkawari a gaban jama’a.

Sanusi Garba Rikiji a lokacin da ya fara gabatar da jawabinsa ya ce hakika 2nd Lieutenant Abdurrahman Abdullahi, ka Sanya mu murna da farin ciki da wannan kokarin kammala karatun Sojan da ka yi.

“Wannan abin da muke yin bikin nan a yau suk sakamakon kokari da jajircewarka tare da mayar da hankali da kuma sadaukarwa da ka yi  ne duk da irin tsananin wahalar da ke tattare da wannan karatu da samun horon Soja a makarantar horas da Sojoji ta NDA don haka muke taya ka murnar zama Sojan Najeriya”.

Rikiji ya kuma bukaci daukacin wadanda suka halarci wannan taron Walimar taya murnar da kowa ya tashi a kalla na minti daya domin girmamawa da addu’a ga marigayi Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi Walin Shinkafi.

” Yau kwanaki Casa’in da Tara (99) kenan da rasuwar marigayi Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi, amma a shekarar da ta gabata muna nan tare da shi a dai wannan wurin domin gudanar da Walima makamanciyar wannan   kuma shi ne Bako mai jawabi, kuma kamar yadda na san Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi tun daga wannan ranar yake ta kokarin yin shirin wannan rana ta yau dinnan da muke gudanar da wannan taro amma Allah bai nufa ba”.

Rikiji ya ci gaba da bayanin cewa amma dai kamar yadda kowa ya Sani cewa duk irin shiri da tsarin da mutum ke yi tsarin Allah ubangiji ne ya fi domin shi ne fiyayye, saboda haka nake tabbatarwa da jama’a cewa ina da yakinin idan da Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi na da rai zai kasance da mu a nan Allah ya gafarta masa.

Sai kuma ya gayyaci wadanda suka kammala samun horon zama Sojojin su biyu da daya daga ciki dan sa ne na cikinsa sai kuma da ya bayyana su da cewa sun yi karatu a wuri daya sun samu horon Soja a wuri daya kuma sun kammala an kuma tabbatar da su a matsayin sojojin Najeriya a matsayin 2nd Lieutenant da ya bayyana su da cewa suna da wadansu abubuwa masu kama daya da suka hada da tsawonsu, da Hancinsu inda a nan take ya gabatar da su a gaban jama’a tare da tambayar jama’ar cewa kun ga hakan ko?

“Lieutenant Abdulkadir Abdulkadir Sani cewa akwai kyakkyawar dangantakar da ke a tsakanin mu a matakin iyalina baki da na marigayi Farfesa Abdullahi Shinkafi a matsayin mu na iyayenku kafin marigayi Farfesa Abdullahi Shinkafi ya rasu kun san irin kyakkyawar dangantaka da ke a tsakanin mu don haka ina son ku dauki alkawari a gaba na da sauran jama’ar da ke na a yau cewa zaku yi Mani alkawari kuma zaku yi wa kowa alkairi da ke wannan wurin cewa kyakkyawar dangantakar da kuka gani kuma a yau kuka gaje ta daga wurin mu cewa zaku rike wannan dangantakar ku kara ingantata a matsayinku na Sojojin Najeriya, kun yi Mani alkawari?

“Ni a matsayina na Sanusi Garba Rikiji na dauki alkawari tare da rantsuwa cewa zan ci gaba da rike hannayen ku a matsayin Tagwaye iyakar iyawata na abin da zan iya yi har tsawon abin da ya rage na rayuwata kuma ina yin addu’ar cewa wata rana Allah madaukakin Sarki zai mayar da ku Janaral na Soja Kuma ina tabbatarwa da mutanen Jihar Zamfara masu karamci cewa da ikon Allah an haifi manya manyan Sojoji da za su kasance Janaral daga Jihar Zamfara in Allah ya so kuma sun fito ne daga iyalai daya, sun samu horon Soja iri daya daga Jiha daya, idan zaku iya tunawa an samu ainihin janarori guda biyu daga iyalan bamai yi daga Jihar Kebbi don haka muma Allah ya ba mu na mu a yau a Jihar Zamfara da ikon Allah.

Da yake tofa albarkacin bakinsa tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Muktar Ahmad Anka, fatan alkairi ya yi wa Abdurrahmad Abdullahi Shinkafi bisa kammala karatunsa da ya yi a makarantar horar da hafsoshin Sojoji ta NDA.

Sai ya yi kira ga daukacin al’ummar Najeriya da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga jami’an tsaro domin tabbatar da tsaron kasa da dukiyar jama’a. Ya kuma jinjina da Yabo ga Honarabul Sanusi Garba Rikiji da ya shirya wannan taro domin a taya Abdurrahman Abdullahi Shinkafi murnar kammala karatu lafiya daga makarantar horar da jami’an Sojoji ta kasa.

Daga hagu Sanusi Garba Rikiji ne sai tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Mahmuda Aliyu Shinlafi, Sai kuma 2nd Lieutenant Abdurrahman Abdullahi Shinkafi da kuma Alkalin babbar kotun Jihar Zamfara (High court)Alkali Bello Muhammad Shinkafi suke yanka kak domin murnar kammala karatun da Abdurrahman ya yi na zama sojan Najeriya.

Daga cikin wadanda suka halarci wannan taron akwai manyan janarori na Soja da kuma iyalan wadannan suka kammala karatun da suka hada da Kakarsa da sauran yan uwa Maza da Mata musamman ma dai al’ummar karamar hukumar Shinkafi da suka yi turuwa saga garin Shinkafi da wasu kuma mutanen Shinkafi da ke zaune a cikin garin Gusau da na Abuja da sauran wurare a ciki da wajen Najeriya da suka ta ya Abdurrahman Abdullahi Shinkafi murnar kammala karatun soja da ya fito a matsayin 2nd Lieutenant a mukamin Sojan Najeriya.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.