Home / Labarai / Matakin Da Na Dauka Na Barin PDP Ne  Mafi Alkairi A Yanzu –  Muktar Ramalan Yero

Matakin Da Na Dauka Na Barin PDP Ne  Mafi Alkairi A Yanzu –  Muktar Ramalan Yero

Daga Imrana Abdullahi

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Dokta Ramalan Yero ya bayyana cewa matakin da ya dauka na barin PDP ne abu mafi alkairi musamman a gare shi da magoya bayansa baki daya.

Muktar Ramalan Yero ya bayyana hakan ne a wani sakon murya da aka aike mana ta kafar Sada zuminta ta “Whattsapp” inda tsohon Gwamnan na Kaduna, ya ce ya na ba masoya da magoya bayansa hakuri bisa matakin da ya dauka.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ” hakika sanarwar ficewa daga jam’iyyar PDP da jama’a suka ga sanarwa gaskiya ne don haka ina yi wa Allah godiya kuma ina yi wa ita kanta jam’iyyar godiya da damar da na samu a cikin ta na rike matsayi daban daban wannan jam’iyya da matsayi da duk matakan da na rike a cikin ta, wata kila ta yuwu iyakar zama na a cikin jam’iyyar kenan kasancewar komai na da farko kuma ya na da karshe kai hatta ita kanta duniyar ma akwai lokacin da za a wayi gari babu ita. Ko mu kanmu akwai ranar da za a wayi gari babu mu baki daya, na bari a cikin mutunci da salama”.

Ina son in roki masoya da magoya baya da su yi hakuri da wannan matakin da na dauka da nake ganin shi ne mafi alkairi a gare mu baki daya kuma a nan gaba zan fito in yi bayani a kan makomar siyasa ta na ko in ci gaba da yin siyasar ko- in barta ma baki daya ko kuma ma ga abin da zan yi, na gode kwarai da gaske na gode da goyon baya, assalamu alaikum”.

Sai dai tsohon Gwamna Muktar Ramalan Yero ya ci gaba da bayanin cewa akwai jam’iyyu da yawa da a can baya suka tuntube shi kuma ko a yanzu ma ana tuntubarsa.

About andiya

Check Also

Aliyu Sokoto tasks cabinet on transformation drive, ‘ be committed and sincere 

  By Suleiman Adamu, Sokoto SOKOTO state Governor Dr Ahmed Aliyu Sokoto has tasked members …

Leave a Reply

Your email address will not be published.