Related Articles
Ana Asarar Kashi 60 Na Kudin Shigar Nijeriya – Inji Garba Shehu
Imrana Abdullahi
Mai magana da yawun shugaban tarayyar Nijeriya Malam Garba Shehu ya bayyana cewa sakamakon matsalar cutar Korona da ta haddasa lalacewar tattalin arzikin duniya yasa a halin yanzu kashi 60 na kudin shiga sun daina bamuwa a tarayyar ta Nijeriya.
Garba Shehu ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta bbc hausa, inda ya ce kamar yadda Muhammadu Buhari yake cewa kashi 60 na kudin shigar Nijeriya duk sun daina shiga domin ba a samun kudin sakamakon lalacewar tattalin arziki a kasashen duniya.
Saboda haka ba ta yadda za a yi mutum ko Gwamnati ta bayar da abin da bata dashi.
“Muna kira ga jama’a da a daure a rungumi abin da yazo a halin yanzu na wannan karin farashin mai da ya tashi a duniya, Lamar yadda a zamanin tsakiyar yaki da cutar Korona aka samu saukin farashin mai kuma kowa ya amfana, don haka ayi hakuri a rungumi tashin farashi ko rayuwarsa
Ya ci gaba da cewa ” Kasashe da dama a duniya in banda kasar Caina its kadai ce tattalin arzikinta ya karu da kashi uku bisa dari, amma kasashe irinsu Amurka da Ingila sun samu raguwar tattalin arziki da kashi Ashirin da wani abu zuwa Talatin don haka sai an yi hakuri.
Garba Shehu ya bayar da misali da kasashe irinsu Ghana da Nijar da ke da Man Fetur amma basa sayar da litar mai kasa da naira dari uku har zuwa Dari uku da Tamanin