Related Articles
Ana Karbar Harajin Da Ya Wuce Hankali A Abuja – Adamu Hassan
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban kungiyar yan kasuwa ta Arewacin Nijeriya Alhaji Adamu Hassan ya bayyana cewa ana matsawa yan kasuwa da karbar haraji duk wata a hannun kananan yan kasuwa.
Adamu Hassan ya ce ana karbar kudin da suka kai naira dubu 10 duk wata daga yan kasuwar da suke sana’a cikin yan kananan rumfuna a birnin tarayya Abuja da sunan kudin wata wata da ake kira da ( service charge).
Saboda haka ya yi kira ga Gwamnati da ta rika duba irin wadannan abubuwan musamman ganin cewa yan kasuwa na taimakawa wajen ciyar da kasa gaba.
Adamu Hassan ya ci gaba da cewa idan aka je yankin arewacin Nijeriya a Jihar Borno a halin da ake ciki mutum dan kasuwa mai jarin naira miliyan 10 ko miliyan 20 yanzu bashi da dubu 20 tashi ta kansa ya gudu ya bar yayansa, gida, mata, motarsa da duk abin da ya mallaka ya koma sansanin yan gudun hijira, to, wa ya dace a taimakawa in ba irin wadannan mutanen ba?
Adamu ya kuma yi kira ga Gwamnati da ta yi tunani a game da wadansu kayayyakin da ya dace a fitar da su daga Nijeriya domin akwai muhimmanci kwarai ga ciyar da kasa gaba.
Kamar yadda Alhaji Adamu Hassan ya bayyana cewa ana karbar harajin ne da sunan kudin wata wata ( Service charge).