Home / Labarai / Ana Son Haifar Da Rigima Tsakanin Fulani Da Al’ummar Hausawa Ne – Bayero

Ana Son Haifar Da Rigima Tsakanin Fulani Da Al’ummar Hausawa Ne – Bayero

Ana Son Haifar Da Rigima Tsakanin Fulani Da Al’ummar Hausawa Ne – Bayero
Mustapha Imrana Abdullahi
Mataimakin shugaban kungiyar matasan al’ummar Fulani ta kasa Alhaji Abdulkarim Bayero ya bayyana wa manema labarai cewa sakamakon irin kyakkyawan binciken da suka gudanar ya tabbatar masu cewa ana yi wa jama’ar yankin arewacin Nijeriya tarko ne ta yadda za a lalata yankin baki daya.
Ita dai kungiyar mai suna Fulbe Ummiobe Sukabe Development Association of Nigeria ( FASADAN) an samar da ita ne domin ciyar da kasa gaba, musamman ta fuskar wayarwa da daukacin al’umma da kai a game da abubuwan da suka shafi ci gaban rayuwa baki daya.
Bayero ya ci gaba da cewa suna nan za su fara aikin zuwa wurare domin wayarwa yan uwa Fulani da kai a game da abin da ya shafi harkokin rayuwa ta fuskar Ilimi, al’amuran rayuwa baki daya.
“Mun gano wani al’amarin da a halin yanzu sai mun tashi tsaye mu jama’ar arewacin Nijeriya saboda irin yadda ake kokarin wargaza yankin Arewa amma hakan ba zai samu ba sai an hada fitina tsakanin al’ummar Fulani da Hausawan Arewa baki daya, kuma Allah ya taimake mu mun fahimci hakan shi yasa muke fadakar da jama’a”, inji mataimakin shugaba Bayero.
Ya ci gaba da bayanin cewa “zamu fara shirin fadakarwa ga al’ummar Fulani domin su fahimci yadda al’amuran suke tafiya a kasa baki daya,
Muna kira ga Gwamnatin tarayya da sauran Jihohin kasar nan da su Sani cewa babu inda ba batagari a cikin al’umma don haka ya dace a dauki muhimmi da zai kawo warwarewar matsaloli a kasa.
Kasancewa akwai masu matsala yan kalilan a cikin Fulani ba shi ne ke Alamta cewa duk Fulani suna da matsala ba.
A wajen dan kwarya kwaryar taron dai an bayar da tabbacin kafa wata kungiyar yan banga ta Matasa domin kawo gudunmawa a samu nasarar da ake bukata kasa ta ci gaba.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.