Home / News / Ana Zargin Wani Sanata Da Kokarin Cire Shugaban Majalisar Dokokin Jigawa

Ana Zargin Wani Sanata Da Kokarin Cire Shugaban Majalisar Dokokin Jigawa

Wani Sanatan da ake zargi da kokarin cire shugaban majalisar dokokin Jihar Jigawa da ke Arewacin tarayyar Nijeriya ya kaddamar da yekuwar dawo wa daga rakiyar shugaban majalisar.
Ana zargin dan majalisar Dattawan ne da kokarin batawa shugaban majalisar suna ta hanyar yin kalaman da za su Sanya a dawo daga rakiyarsa wanda hakan ka iya sanyawa a fara kokarin Tsige honarabul Garba Idris Jahun,a matsayin shugaban majalisar dokokin Jihar Jigawa
Ana dai ganin Sanatan na kokarin zama Gwamnan Jihar Jigawa ne a shekarar 2023 wanda hakan ya sa ake zarginsa da kokarin bata sunan shugaban majalisar dokokin na Jihar Jigawa ta hanyar yin amfani da wasu yan majalisar dokokin su fara shirin cire shi daga kan kujerar shugaban majalisar dokokin na Jihar Jigawa duk kuma wannan na faruwa ne bayan ya kasa shawo kan Gwamna Badaru ya amince da hakan a yan makonnin da suka gabata.
Taron da aka yi a kwanan nan da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga mazabarsa (sanata), an yi taron ne a gidansa kamar yadda wani da ya nemi kada a ambaci sunansa ya shaidawa majiyarmu, inda ya tabbatar mana cewa Sanatan ya fito fili ya shaida masu cewa zai dukkan abin da zai iya domin cire shugaban majalisar daga kan kujerar shugabancin majalisar domin kawai ya ki amincewa da ya gayi bayan Sanata a matsayin wanda ya fi cancantar ya Gaji Gwamna Badaru idan wa’adin Muslinsa ya kare a shekarar 2023.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, ana ganin shugaban majalisar dokokin na Jihar Jigawa a matsayin mai goyon bayan Gwamna Badaru, wato dan gani kashenin Gwamnan don haka ba zai amince ya go yi bayan kowa ba ko wani rukunin yan siyasa ba a Jihar Jigawa.
Wasu majiyoyi masu inganci sun tabbatar da cewa wannan aikin kokarin cire shugaban majalisar ya fara ne daga wani dan majalisa daga mazabar Ringim, honarabul Aminu Sule Sankara wanda shi ake zargi da yin jagorancin wannan aikin cire shugaban majalisar ya na kuma kokarin samo hadin kan wadansu yan majalisar domin su amince su kuma aikata aikin a madadin Sanatan.
Akwai wadansu alamun cewa Sanatan dai a lokacin da wannan rikicin ya kawo tsakiya ya na ganin shugaban majalisar dokokin Jihar Jigawa a matsayin wata barazana a gare shi dangane da kokarinsa na zama Gwamnan Jihar Jigawa saboda kawai shugaban majalisar ya tsaya kaifi daya mai goyon bayan Gwamna Badaru wanda kuma aka amince da shi a hakan wanda hakan zai iya sanyawa ya zama cikin mutanen da za su tabbatar da wanda zai ga ji Gwamna Badaru idan wa’adin Mullinsa ya kare.
Wata majiyar kuma da ta kasance wani dan majalisa ne na Jihar Jigawa wanda ya shaida mana cewa tuni Gwamna Badaru ya ki amincewa da wannan bukatar cire shugaban majalisar kuma ya bayyana goyon bayansa ga shugaban majalisar dokokin na Jigawa.
Saboda hakan a halin yanzu ake ganin Sanatan da kuma wasu daga cikin masu goya masa baya suke kokarin lalubo wanda za a maye gurbin shugaban majalisar dokokin na Jigawa, musamman daga cikin wadanda suka karbi kudi daga Sanatan da za su yi aiki cewa sun Tsige shugaban majalisar dokokin a cikin majalisar dokokin Jihar Jigawa idan ta zauna idan an dai- daita komai a cikin sati mai zuwa inji majiyar da ta nemi a sakaya sunanta.
Kamar yadda majiyarmu ta shaida mana bayan halartar taron da aka yi, yan kwanaki kadan da suka gabata a gidan dan malisar dattawan (Sanata) cewa akwai alamun mika sunayen mutane biyu da suka hada da Musa Suleiman daga mazabar Dutse ko kuma Honarabul Isah Idris Gwaram domin maye gurbin shugaban majalisar bayan an cire shi daga shugabancin majalisar dokokin ta Jigawa.
 Ya zuwa yanzu dai babu wani bayani ko alama daga wajen Gwamnatin Jiha a game da wannan lamarin.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.