Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna Alhaji Yaro Makama Rigachikun ya bayyana dalilin fitowar tsohon shugaban majalisar Dattawan Najeriya Mista Anyim Pius Anyim domin neman kujerar shugabancin kasar, inda ya ce ya fito ne domin hadin kan al’ummar kasar baki daya.
Alhaji Yaro Makama ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da fara fafutukar neman jama’a da aka yi a gidan tunawa da marigayi Sardaunan Sakkwato da ake kira da “area house” kaduna.
Yaro Makama ya ce ya na kaddamar da bude wannan tafiya ne ta tsohon shugaban majalisar Dattawan Najeriya Anyim Pius Anyim domin neman kujerar shugaban kasa bisa cancantar ilimi da kuma gogewar aiki da ya dade ya na yi tsawon lokaci.
“Saboda haka ina tabbatar maku da cewa bisa sanin da na yi masa ya fito neman kujerar shugabancin kasar nan ne domin tabbatar da hadin kai da taimakon Juna a duk fadin kasa baki daya don haka idan an bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Anyim Pius Anyim ba za a samu wata matsala ba sai dai samun ci gaba da kowa ke bukatar samu”.
Ya kuma yi kira ga dan takarar da ya ci gaba da jajircewa bisa rawanin da ya nada domin neman wannan kujerar ta shugaban kasa har sai an samu bukatar hakan.
Taron dai an yi shi ne a karkashin jagorancin gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu na “Arewa Concerned Civil Society Organization Of Nigeria (ACCSON)”.
Yaro Makama, ya kuma yi kira ga matasa da ake ganin su ne manyan gobe da su daina yin aikin da zai amfana su domin kudi kawai, saboda aiki don kudi kawai akwai dimbin abubuwa a boye, da suka saba da ciyar da kasa gaba.
Makama, ya kuma bayar da sako ga wadanda dan takarar ya aiko Kaduna da su gaya masa gaskiya a game da wannan kokarin da ya fara na nada rawanin takara da kada a kwance rawanin har sai an samu biyan bukata.
Taron dai ya samu halartar dimbin mutane a ciki da wajen Jihar Kaduna musamman daga bangaren matasa da kuma yayan kungiyoyi masu zaman kansu.
An yi taro lafiya an kammala lafiya.