DAGA IMRANA ABDULLAHI
Shugaban kasar tarayyar Najeriya M7hammadu Buhari ya bayar da hakuri ga daukacin al’ummar Jihar Katsina da su yi hakuri su zabi jam’iyyar APC a zaben Gwamnoni da na yan majalisar Jiha mai zuwa
Muhammadu Buhari ya bayyana dan takarar Gwamnan Jihar Katsina Dokta Dikko Umar Radda a matsayin kwararren mutum mai dimbin basira dabzai yi amfani da kwarewarsa wajen ciyar da Jihar Katsina gaba.
Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon faifan bidiyon da ya aikewa jama’a inda yake bayar da hakuri ga jama’ar cewa batun lamarin sake Fasalin kudi da aka yi a halin yanzu ba an yi bane da gangan.
Jama’ a dai na ta tofa albarkacin bakinsu game da wannan bidiyon na shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yazo ne tun bayan da jama’ar Jihar suka bayyana matsayinsu a zaben shugaban kasa da yan majalisun Dattawa da na tarayya, shi yasa ake ganin Buhari tare da wadanda suka san dadin Gwamnati a matakan Jiha da na kasa suke ganin ya dace aba jama’a hakuri su ci gaba da zaben APC da Buhari yake ciki.