Home / Labarai / Ba Dan Makarantar Da Aka Sace A Birnin Gwari – Kwamishina Aruwan

Ba Dan Makarantar Da Aka Sace A Birnin Gwari – Kwamishina Aruwan

Ba Dan Makarantar Da Aka Sace A Birnin Gwari – Kwamishina Aruwan
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana samun wadansu yara guda biyu Namiji da Mace da aka tsincesu cikin Daji suna gararamba.
Su dai wadannan yara biyu masu suna Fatima Lawal mai shekaru 15 da kuma Adewale Razak da suka samu kubuta daga hannun masu Garkuwa da mutane, kamar yadda Fatima Lawal ta bayyana wa manema labarai cewa ta tsinci kanta ne a cikin wannan hali sati uku da ya gabata.
A wajen wani taron manema labarai da ya gudana a Kaduna Kwamishinan kula da harkokin cikin gida da tsaro na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan, ya bayyana cewa biyo bayan irin sanarwar da suka yi da safiyar yau game da daliban Firamare a Birnin Gwari.
A halin da ake ciki tuni Gwamnatin ta kammala tattara bayanai kuma ta samu cewa mutane uku daga cikin Malaman Firamare ta Rema da ke yankin mazabar Magajin Gari ta biyu masu Garkuwa da mutane suka tafi da su.
Malaman makarantar da aka kama sun hada da Rabiu Salisu, Umar Hassan da Bala Adamu. Kuma bayanan sun tabbatar da cewa babu wani yaro dalibi cikin yan makarantar Firamaren da aka kama.
Sai dai kawai daliban da suka halarci makarantar sun samu kansu cikin wani hargitsi ne sakamakon harin da maharan suka kai a kan Babura, yanayin da aka shiga a makarantar ya yi sanadiyyar rashin samun dalibai guda biyu da suka hada da
Ahmad Halilu da Kabiru Yahaya, amma a halin yanzu duk an gansu cikin koshin lafiya da walwala.
 
Rahotannin tsaro da Gwamnatin Gwamnatin samu sun bayyana mata cewa wadansu mahara sun sace shanu,Babura biyar da sauran kayayyaki da dama.
 
Kwamishinan ya ci gaba da bayanin cewa wadansu sojojin Nijeriya da ke aikin sintiri a cikin Dajin kananan hukumomin  Kachiya da Kauru sun yi nasarar tsintar wata yarinya mai suna Fatima Lawal da ta kubuta daga yan bindiga. Kuma kamar yadda bayaninta ya nuna cewa an sace ta ne sati uku da suka gabata a wani kauye mai suna Randa, a yankin Kadage, karamar hukumar Kauru duk cikin Jihar Kaduna.
 
 
Kuma tuni aka mika wadannan yara a hannun iyalansu ta hannun shugabannin kananan hukumomin Chikun da Kauru.
Sai kuma wadansu jami’an sojan da ke aikin sintiri a Faka da ke karamar hukumar Chikun sun tsinci wani saurayi mai shekaru 14 da ke gararamba a cikin dajin Faka da ya bayyana masu cewa sunansa Adewale Rasaq, da aka sace sama da sati daya a unguwar Kudenden a karamar hukumar Chikun, wanda ya ce ana ta dai-daitawa da iyayensa kan a biya kudi naira miliyan 15 amma ya samu kubuta daga yan bindigar.
A kokarin Gwamnati na ganin ta kakkabe yan Ta’adda tare da ayyukansu a Jihar baki daya ta samar da lambobin wayar ta fi da gidanka ta duk wanda ke da wani bayanin da zai amfanar a samu nasarar samun ingantaccen tsaro.
Ga dai lambobin kamar haka 09034000060,08170189999.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.