Home / Labarai / Ba Mu Amince Da Rufe Hanyar Kaduna Zuwa Abuja Ba – Gwamnatin Kaduna
Executive Governor of Kaduna State Nasir El-Rufai speaks during an interview with Reuters in Kaduna, Nigeria November 1, 2016. REUTERS/Afolabi Sotunde - S1BEUKTKGYAA

Ba Mu Amince Da Rufe Hanyar Kaduna Zuwa Abuja Ba – Gwamnatin Kaduna

Imrana Abdullahi Daga Kaduna
-Jami’an Tsaro Su Dauki Matakin Doka
Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I, ta bayyana rashin amincewarta ga duk wani mutum ko gungun wadansu mutane da ke neman toshe hanyar Kaduna zuwa Abuja da sunan yin Zanga zangar nuna rashin amincewa da wani al’amari.
Gwamnatin ta ce yin duk wata Zanga Zanga a kan wannan titi har a rufe hanyar Kaduna zuwa Abuja karya doka da oda ne kawai.
Gwamnatin ta ci gaba da cewa dukkan wani ko gungun wadansu mutane da ke kokarin daukar irin wannan matakin rufe hanya ya dace su kauracewa yin hakan domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Hakika Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta kokarin tauye wa jama’a hakkin su ba ne idan suna son bayyana rashin jin dadinsu, amma dai ta na duba yanayin zaman lafiya ne da kwanciyar hankalin jama’a wanda shi ne a kan gaba kafin komai.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar mai dauke da sa hannun Malam Samuel Aruwan, Kwamishinan ma’aikatar kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida na Jihar Kaduna.
Takardar ta ci gaba da bayanin cewa hakika akwai matsala da ke tattare da rufe babbar hanya kamar irin wannan ta Abuja zuwa Kaduna, saboda muhimmancinta ya wuce misali.
Don haka ya zama wajibi ga Gwamnatin ta tabbatar da daukar mataki a kan duk wani lamarin da ka iya haifar da tashin tashina a tsakanin jama’a.
Saboda haka Gwamnatin ke yin kira ga daukacin jama’a da su guji shiga cikin duk wata Zanga Zanga mai kama da hakan inda za a tauyewa wadansu mutane hakkin neman abincinsu da kuma tattalin arziki baki daya,domin yin hakan na iya Jefa rayuwar sauran jama’a cikin wani hadari.
Sai sanarwar ta ce hakika ya zama abu mai kyau ga dukkan yan kasa su Sani cewa harkar tsaro aiki ne da za a hada hannu domin samar da shi, domin haka dai daikun mutane, gungun jama’a, kungiyoyi da sauransu ya dace su Sani cewa bayar da hadin kai domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali abu ne mai matukar muhimmanci a koda yaushe.

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.