Home / Big News / Gwamnatin Yobe Ta Gina Tituna  Masu Nisan Kilomita 54.6 A Fadin Kananan Hukumomi 9 A Cikin Shekaru 3

Gwamnatin Yobe Ta Gina Tituna  Masu Nisan Kilomita 54.6 A Fadin Kananan Hukumomi 9 A Cikin Shekaru 3

 

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

 

 

A kokarin da ta ke yi na wadata al’ummomin Jihar da hanyoyin mota birane da yankunan karkara Gwamnatin jihar Yobe ta gina tituna da magudanan ruwa masu nisan  sama da kilomita 54.6 a fadin kananan hukumomi 9 na jihar cikin shekaru 3 na gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Kwamishinan ayyuka na jihar Injiniya Umar Wakil Duddaye ne yayin ganawar sa da manema labarai a babban dakin taro na Mai Mala Buni dake sakatariyar ‘yan Jaridu (NUJ) da ke Damaturu, yadda kwamishinan ya yi karin haske kan wasu nasarorin da gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ta samu.

Injiniya Duddaye ya ce, “A kokarin tunawa da manufofin gwamnatin Gwamna Buni, ma’aikatar ayyuka ta jihar Yobe ta gina tituna da magudanan ruwa a kananan hukumomi 9 na jihar wadanda suka hada da;  Hanyoyi masu nisan kilomita 2.0km da magudanan ruwa a rukunin gidajen Zanna Zakariya, da masu nisan kilomita 2.5km a rukunin gidajen Obasanjo, Malam Matari, Gujba Road, da mai nisan kilomita 5.7km da ta tashi daga  NTA Damaturu zuwa hanyar Gujba cikin garin Damaturu hade da magudanin ruwa masu nisan kilomita 15 wadda suka hada har da hanyar da aka gina a cikin   kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma ta Shehu Sule ta Damaturu.

Sauran su ne;  Titi mai nisan kilomita 4.2 daga titin Gashua zuwa Nana Aisha bypass da titi mai nisan kilomita 1.5 tsakanin sakatariyar jiha a Damaturu, titin mai nisan kilomita 3.8 kusa da New Bra-Bra, Estate Nyanya duk a karamar hukumar Damaturu.

Ya kuma bayyana cewa an gina tituna da magudanan ruwa mai tsawon kilomita 2.7 a cikin garin Potiskum.

Haka kuma an gina tituna da magudanan ruwa masu tsawon kilomita 3.7 a cikin garin Nguru da titin kilomita 2.0 da magudanun ruwa a cikin Garin Geidam a karamar hukumar Gaidam.

Ya ce, “An gina tituna da magudanan ruwa na kilomita 2.0 a cikin garin Gashua, titin kilomita 2.3 da magudanun ruwa a cikin garin Jajimaji, titin kilomita 4.0 da magudanan ruwa a cikin garin Buni Yadi da kuma titi mai nisan kilomita 1.6 da magudanun ruwa a cikin garin Babbangida a karamar hukumar Tarmuwa.

Kwamishinan ya kuma  bayyana cewa an kammala dukkan ayyukan tare da saukaka zirga-zirgar kayayyaki da ayyuka a kananan hukumomin jihar.

“Kokarin da wannan ma’aikatar ta ke yi na kara kaimi ga kokarin gwamnatin jihar wajen samar da dauki cikin gaggawa da kuma magance matsalar ambaliyar ruwa da aka saba yi a baya-bayan nan gwamnatin Buni ba za ta gajiya ba kan hakan in Allah ya so.”

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.