Home / Labarai / Ba Mu Ce Muna Neman Matawalle Ruwa A Jallo Ba – EFCC 

Ba Mu Ce Muna Neman Matawalle Ruwa A Jallo Ba – EFCC 

Sabanin irin yadda ake ta yada wadansu rahotanni marasa tushe balantana makama  cewa wai Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) na neman tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ruwa a jallo, wanda kuma ba hakan bane.

 Hukumar Efcc ta musanta rahotannin da ake yadawa a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa ta bayyana tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, wanda ake nema ruwa a jallo, sam ba haka bane.

Wata jarida da ba theshieldg.com ba ta ruwaito cewa hukumar ta bayyana Bello Muhammad cewa ana neman sa a kan naira biliyan 70 da ake zarginsa da almundahana.

Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Mista Wilson Uwujaren ya fitar a ranar Lahadin nan ta ce har yanzu hukumar ba ta bayyana tsohon gwamnan ba, kuma ba ta nemi taimakon wata hukuma ciki har da DSS don aiwatar da nasa aikin ba.

“An jawo hankalin Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, kan wani rahoto, mai taken, Zargin almundahanar Naira biliyan 70: EFCC ta bayyana tsohon Gwamnan Zamfara, Matawalle, wanda ya bayyana a jaridar Sunday Tribune ta ranar 18 ga watan Yuni, 2023 da kuma zarginsa.

Hukumar ta bayyana cewa, wani tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, muna nemansa ruwa a jallo, ta kuma bukaci hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, da ta kama shi, “duk inda aka gan shi”.

“Ba tare da nuna kyama ga shari’ar da ta shafi tsohon gwamnan ba, rahoton ba daidai ba ne domin har yanzu Hukumar ba ta bayyana Matawalle ba ko kuma ta nemi taimakon wata hukuma ciki har da DSS don kama shi ba.

Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar tana da daidaitaccen tsari na bayyana wadanda ake nema da kuma sadarwa da jama’a, ba ta hanyar “majiyoyin tsaro marasa fuska ba,” in ji sanarwar.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.