Home / Labarai / AN MIKAWA KOTU MOTOCIN MATAWALLE – YAN SANDA

AN MIKAWA KOTU MOTOCIN MATAWALLE – YAN SANDA

Duk motocin da rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta kwace daga hannun tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle, an mikawa kotu ne a ranar Asabar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar din da ta gabata ta wata tattaunawa ta wayar tarho, inda ya ce an mayar da motocin ne bisa bin umarnin babbar kotun tarayya da ke Gusau.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Aminu Bappah-Aliyu, ta umurci dukkanin hukumomin tsaron da suka kwashe motocin daga gidajen Matawalle da ke Gusau da Maradun da su dawo da su cikin sa’o’i 48.

Sai dai kamar yadda jami’an yan Sanda suka bayyana cewa a bisa umarnin gwamnatin jihar, jami’an tsaro sun kwashe motocin daga gidajen tsohon gwamnan biyu.

A cewar Abubakar, “Eh, rundunar ‘yan sanda ta bi umarnin kotu dangane da mayar da dukkan motocin tsohon gwamna Bello Matawalle.” Inji Abubakar.

Ya kuma bada tabbacin cewa an mayar da dukkan motocin zuwa harabar babbar kotun tarayya da ke Gusau.

Kakakin Gwamna Dauda Lawal na Zamfara, Suleiman Idris, ya ce tun farko an kwato motoci fiye da 40 daga gidajen tsohon gwamnan biyu.

Ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro sun dauki matakin ne bisa umarnin gwamnatin Jihar.

About andiya

Check Also

Dangote cement export of clinker, cement increase by 87.2%

  Management of Dangote Cement Plc has revealed that the company dispatched seven ships of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.