Home / Labarai / Ba Za A Daina Amfani Da Tsofaffin Takardun Kudi Ba -CBN

Ba Za A Daina Amfani Da Tsofaffin Takardun Kudi Ba -CBN

Daga Imrana Abdullahi

….A Ci Gaba Da Karbar Takardun kudi A Najeriya

 Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa babu tsarin daina yin amfani da tsofaffin takardun kudi a duk fadin tarayyar Najeriya don haka kalaman da wasu ke yadawa jita – jita ce kawai babu wani kamshin gaskiya a ciki domin batun ba daga babban Bankin ba ne.

Babban Bankin ya dai tabbatar da hakan ne a cikin wata takardar da ya fitar mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai na babban Bankin Isa Abdulmumin da aka rabawa manema labarai.

A cikin wannan takardar dai babban Bankin ya tabbatarwa manema labarai domin su sanar da duniya cewa batun da wasu ke yadawa cewa a daina amfani da tsofaffin takardun naira kamar na Dubu daya da dari biyu duk zancen shaci fadi ne kawai don haka kowa ya ci gaba da hidimarsa kamar yadda ya saba da tsofaffin takardun kudin wato masu sana’a su ci gaba da karba su kuma masu sayayyar kaya su ci gaba da yin amfani da su suna karba a hannun jama’a.

 

Haka zalika babban Bankin ya kuma ce (CBN) ya sake tabbatar wa al’ummar ƙasar cewa akwai isassun takardun kuɗi na Naira tare da kwantar da hankalin mutane na daina shiga firgici saboda ƙarancin kuɗaɗe a bankuna.

Babban bankin, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ta hannun Kakakin sa, Isah Abdulmumin, ya sake nanata cewa tsofaffi da sabbin takardun kuɗi na Naira suna daram.

“Don kaucewa shakku, muna nanata cewa akwai isassun takardun kuɗi a faɗin ƙasar nan don gudanar da duk harkokin tattalin arziki na yau da kullum,” in ji kakakin CBN, Isa AbdulMumin.

“Saboda haka, an umarci rassan bankin CBN a faɗin ƙasar nan da su ci gaba da fitar da takardun kuɗi daban-daban na tsofaffi da sabbi cikin adadi mai yawa zuwa bankunan kasuwanci don ci gaba da rarrabawa ga abokan huldar bankuna.

“Muna so mu sake bayyana cewa duk takardun kuɗi na banki da CBN ke bayarwa suna nan a kan doka. Kamar yadda sashe na 20 (5) na dokar CBN ta shekarar 2007, babu wanda ya isa ya ƙi karɓar Naira a matsayin hanyar biyan kuɗi.”

CBN “ya sake tabbatar da cewa akwai isassun takardun kuɗi don sauƙaƙa ayyukan tattalin arziki na yau da kullum”.

In dai za iya tunawa, watan Oktobar shekarar da ta gabata ne tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana shirin sake fasalin wasu kuɗaɗe, sannan ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su musanya tsofaffin takardunsu kafin ranar 31 ga watan Junairu, 2023.

Wannan hukunci ya haifar da taɓarɓarewar tattalin arziki yayin da ‘yan Nijeriya da dama suka shiga mawuyacin hali, lamarin da ya haifar da tarzoma a wasu jihohin da kone wasu bankuna da kuma injinan cire kuɗi

About andiya

Check Also

Dangote cement export of clinker, cement increase by 87.2%

  Management of Dangote Cement Plc has revealed that the company dispatched seven ships of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.