Home / Labarai / Ka Rabu Da Matawalle Daga Batun Gazawarka, Kungiyar AYCF Ta Gargadi Gwamnan Zamfara

Ka Rabu Da Matawalle Daga Batun Gazawarka, Kungiyar AYCF Ta Gargadi Gwamnan Zamfara

 

Kungiyar tuntuba ta matasan arewacin Najeriya karkashin jagorancin shugaba na kasa Shettima Yerima ta yi gargadi ga Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal a kan cewa ya dace ya rabu da ministan tsaro Muhammad Bello Matawalle a game da batun gazawarsa a wajen yin jagorancin Jihar.

Kamar yadda kungiyar ta bayyana a cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai cewa Gwamna Dauda na yin amfani da sunan mutumin da ya gada wato Bello Muhammad Matawalle, wanda a yanzu shi ne ministan kasa a ma’aikatar tsaro don kawai Dauda Lawal ya gaza yin komai a Jihar.

 

 

 

Kungiyar a cikin wata sanarwar da suka fitar mai dauke da da hannun shugaba Yerima Shettima inda suka ce hakika irin yadda Dauda Lawal ke aikatawa ma wai ba wai zai dakushe Jihar ba ne kawai har ma da al’ummarta baki daya.

 

 

“Irin yadda Dauda Lawal a kullum ke ambaton sunan Matawalle a matsayin wata Garkuwa na yadda ya gaza aiwatar da komai a Jihar musamman ta fuskar samar da tsaron dukiya da lafiyar jama’a a fili lamarin yake cewa ya gaza daukar nauyin yadda ya gaza musamman a kan abin da yake yi.

 

 

“Mun gargadi Dauda Lawal, ya Sani cewa muna nan a kan kokarin samun muhimman shaidun da za a dogara da su na makudan kudin da ya yaki shugaba Bola Tinubu da irin kamfe din da ya aiwatar musamman a game da batun shaidar karatun shugaban kasa a Chikago don haka ba zamu yi kasa a Gwiwa ba wajen Fallasa yadda batun yake,musamman idan ya dage a kan sai ya dakushe martaba da darajar Gwamnatin tarayya da kuma rabawa ta gefen ministan kasa a ma’aikatar tsaro.

 

 

” A kan haka ne muke yin kira ga shugaban kasa Tinubu da ya duba inda aka fito can baya a game da abin da wasu ke aikatawa a gidan Gwamnatin jihar Zamfara da suke yin dukkan abin da za su iya sai sun haifar da matsala ga nasarar da Gwamnatin tarayya ke samu”, inji Shettima.

 

Ya ce madadin yin kokarin magance matsalar tsaron da ake fuskanta a Jihar, sai kawai Lawal ke yin amfani da sunan mutumin da ya gada wajen Dora masa laifi da kuma gaza aiwatar da komai a Jihar musamman ta fuskar gaskiya da adalci a kan harkar kudi. Wannan halin ba wai ya na haifar da matsala ba ne wajen tabbatar da gaskiyar al’ummar Jihar har ma ya na haifar da nakasun samun ci gaba da kuma matakan magance matsalar tsaro a jihar”, duk inji Kungiyar.

 

 

Kamar yadda kungiyar ta ce, babban abin da dukkan wata Gwamnati ya kamata ta aiwatar ga jama’a shi ne batun tsaron lafiya da dukiyarsu, saboda haka ya dace Dauda Lawal ya san wannan.

 

“Kamar yadda kowa ya Sani mulkin Dauda Lawal ya zamo wata matsalar hauhawar matsalar tsaro da suka hada da Satar jama’a, illar yan bindiga da sauran matsalolin tsaro baki daya, a madadin makalewa kawai ana ta harbin iska a kan batutuwa da dama. Sai kawai Lawal ya zabi yin amfani da sunan Matawalle wanda a halin yanzu yake yin aikace aikacen tabbatar da ci gaban kasa a matakai daban daban, amma sai ga Dauda Lawal na kokarin karkatar da wannan tunanin domin ya boye gazawarsa.

 

” Da yin amfani da sunan Matawalle, Gwamna Dauda Lawal ba wai ya na kokarin karkatar da hankalin mutane ba ne kawai har ma ya na kokarin dakushe irin kokarin aikin da ministan kasa a ma’aikatar tsaro yake yi da nufin kada ya mayar da hankali wajen magance matsalar tsaron da ake fama da ita musamman wajen ci gaba da samar da ingantaccen tsaro, wanda hakan da Dauda ke yi na kokarin haifar da matsala game da irin yadda Gwamnatin tarayya ta amince da yarda da Matawalle”, Inji Yerima.

 

 

 

 

Kungiyar ta ci gaba da cewa, abin da Gwamna Lawal ke aikatawa ya shafar jama’ar Jihar, idan aka yi la’akari da gazawarsa wajen magance matsalar tsaro wanda hakan ya haifar da tsananin rashin tabbas a Jihar. Jama’ar sun cancanci samun shugaba da zai dauki nauyin sama masu tsaron lafiya tare da dukiyarsu da kuma yin aikin yadda za a samar da mafita ta karshe game da matsalar tsaron.

 

 

 

 

Wato dai a fili take a yanzu cewa irin yadda Dauda Lawal ke amfani da ambaton sunan Matawalle shaida ce mai nunin cewa babu wani ci gaban da za a kawo.

 

“Muna yin kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu irin abubuwan da Dauda Lawal ke aikatawa wani bangare ne na wani tsarin dakushe irin soyayyar da al’ummar Jihar Zamfara ke yi masa tare da Gwamnatinaa a matakin tarayya da ministan kasa a ma’aikatar tsaro ke kokari wajen kare martaba da mutuncin Gwamnatin tarayya baki daya a koda yaushe”, inji kungiyar.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.