Home / Labarai / Babban Alkalin Jihar Kogi, Mai Shari’a Nasiru Ajana Ya Rasu

Babban Alkalin Jihar Kogi, Mai Shari’a Nasiru Ajana Ya Rasu

Imrana Abdullahi
Rahotannin da ke Iske mu daga garin Abuja na cewa babban mai shari’a na Jihar Kogo a Arewacin tarayyar Nijeriya, mai Shari’a Nasiru Ajanah ya rasu a yau da safiyar Lahadi a Abuja.
Bayanan da ke Iske mu sun bayyana cewa ya rasu ne bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya
Marigayin dai ya fito ne daga karamar hukumar Okehi a cikin Jihar Kogi.
Mai shari’a Nasiru Ajanah ya rasu yana da shekaru 64 a duniya. In dai za a iya tunawa a satin da ya gabata ne Jihar Kogi ta rasa wani babban mai shari’a shugaban kotun daukaka kara a kotunan gargajiya mai shari’a Ibrahim Sha’aibu Atadoga.

About andiya

Check Also

Sokoto APC supporters take over major streets for Aliyu Sokoto’s victory

  By Suleiman Adamu, Sokoto   It has been jubilation all through by thousands of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.