Home / Labarai / A Mayar Da Liman Musa Tanimu Zariya – Al’ummar Unguwar Rimi

A Mayar Da Liman Musa Tanimu Zariya – Al’ummar Unguwar Rimi

Imrana Abdullahi
Al’ummar Unguwar Rimi da ke cikin garin Kaduna a Arewacin tarayyar Nijeriya sun bukaci a mayar da Liman Musa Tanimu Zariya a kan Limancinsa na masallacin babban masallacin unguwar Rimi ( central mosque) da ake kira masallacin iyaye da Kakanni.
Al’ummar ta bakin daya daga cikin wadanda suka yi wa manema labarai jawabi mai suna Muhammad Ahmad, sun bayyanawa manema labarai cewa tun da har fadar mai martaba Sarkin Zazzau ta hannun Hakimin Gabasawa Alhaji Shehu Dikko sun tabbatar cewa wannan Limamin Malam Musa Tanimu Zariya ba dan shi’a bane don haka sai kawai a mayar da shi kan Limancinsa saboda shi jama’a suke bukatar ya yi masu Limancin Sallah a masallacin Iyaye da kakanni.
” Cikin mu yan kwamiti mutane 20 bai wuce mutum biyu, uku zuwa hudu ba suka yi wannan zargin cewa Liman Musa Tanimu Zariya dan Shi’a ne, wanda bincike ya tabbatar ba dan shi’a bane. Kuma su kansu mutanen sun tabbatar a wajen jami’an tsaro cewa sun tuba bisa abin da suka aikata to, me ya rage kawai a mayar da mutumin nan kan kujerarsa kawai”. Inji Muhammad Ahmad.
“A mayar da Liman Musa Tanimu Zariya domin zaman lafiyar unguwar Rimi da mutanenta baki daya”, inji Muhammad Ahmad.
“Son billahi wallahi summa Tallahi Kawhi 97 ko 98 zuwa kashi Dari na mutanen unguwar Rimi suna tare da Malam Musa Tanimu Zariya, saboda na taba yin kira ga mai girma Gwamnan Kaduna cewa idan za a dage dokar hana fita in za a bude masallatai to, jada a bude masallacin iyaye da Kakanni da ke unguwar Rimi”.
“Amma kuma sai ga shi an bude kuma kullum muna Sallah tare da jami’an tsaro, shin a kullum sai da yan sanda zamu yi sallah? Su jami’an tsaron ba su da aikin yi sai  Gadin Masallaci? kowa ya san jami’an tsaro suna da ayyukan yi da yawa”, inji Muhammad Ahmad.
Ya ci gaba da cewa suna yin kira ga hukumomi da Gwamnati da su mayarwa da Limamin masallacin iyaye da kakanni da Limancinsa saboda shi ne addini ya tanadar.
“Ko tafiya za a yi addini ya tanaji cewa mutane su saka shugaban da zai shugabanci su a tafiyar”.
Al’ummar ta unguwar Rimi sun nuna wa manema labarai takardar da Malam Musa Tanimu Zariya ya ta fi kotu domin neman hakkinsa. Kuma in hali ya yi zamu ci gaba da kawo maku yadda lamarin yake kayawa a kotun.

About andiya

Check Also

NASCON grows turnover by 37%, assures Shareholders of Continuous Growth, Value Creation

NASCON Allied Industries Plc has assured its shareholders of continuous growth and value creation in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.