Daga Salisu Na’inna Dambatta
Allah Ya yi ikonsa, ga shi ranar 26 ga watan nan na Maris a wannan shekara ta 2022 za a yi babban taron jam’iyyar APC na kasa. Wannan taro ya kusa zama zahiran domin an kama turba sak domin yin taron lafiya, a gama lafiya.
Shugabancin riko na jam’iyyar APC wanda mai girma gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ke shugabanta ne ya shirya taron. Tuni kwamitin ya kafa kananan kwamitoci 22 domin yin taron cikin nasara. Wannan kuwa ya yi daidai, domin an ce hannu da yawa ne kan dauki jinka.
A can baya, masu son cinna wutar rikici a jam’iyyar APC sun sha yada jita-jita wai ba za a yi taron ba, saboda son biyan bukatar wasu. Wannan zargi kuwa daman janhuru ne, kuma yanzu gaskiya ta bayyana, karya ta kare. Ranar wanka, ba a boyon cibiya.
Wannan taro da za a yi, ya na daya daga cikin irin nasarorin da kwamitin rikon ya samu ne wajen farfado da APC bayan ya magance rikicinta na cikin gida. Domin kafin a kai ga wannan taro, sai da kwamitin rikon ya shirya zaben shugabannin APC a mazabun ungwanni da matakin kananan hukumomi, har aka kai ga na jihohi. Yanzu kuma ga shi za a yi zaben shugabbnin jamiyyar na kasa baki daya.
Wasu nasarorin da APC ta samu a sanadin shugabancin riko na jamiyyar karkashin Alhaji Mai Mala Buni su ne biyan basussukan da ke kan jamiyyar da sayawa jamiyyar ofis na kanta maimakon zaman haya, da warware rigingimu tsakanin ‘yan jam’iyyar, ko tsakaninta da wasu, ciki har da wadanda aka kai gaban masu shari’a. Bayan duk wadannan nasarori, kwamitin ya sulhunta tsakanin ‘ya’yan jamiyyar masu rigima da juna.
A gaskiya ma saboda yadda wasu gaggan ‘yan siyasa ciki har da Gwamnonin Jihohi biyu da ‘yan majalisun dokoki da yawa suka ga yadda kwamitin na Alhaji Mai Mala Buni ke tafiyar da jamiyyar APC cikin tsari mai kyau da kwarewa, sai suka fice daga jamiyyunsu na baya suka, shiga jamiyyar APC. Wannan ya kara wa APC kwarjini da albarka.
Wani babban aiki da kwamitin ya yi, wanda ya zama wata babbar nasara, shine na gyara tsarin mulkin jam’iyyar tare da kirkiro sabbin mukamai yadda za a kara yawan ‘ya’yanta a harkokin mulkinta. Wannan kuwa hikima ce, domin kowa zai ji ana yi da shi. A cikin wannan tsari, an warewa mata da matasa da masu bukatu na musamman mukamai. Yin hakan zai sa jam’iyyar ta ci moriyar basirarsu ta irin gudunmowar da za su bayar a tafiyar da harkokinta.
Haka nan dai a karkashin jagorancin mai girma Alhaji Mai Mala Buni, jamiyyar APC ta sami karin wadanda suka shige ta. A yau din nan APC ta na da ‘ya’ya wadanda ta yi wa rajista fiye da miliyan 41.7 (miliyan arba’in da daya da dubu dari bakwai.). In banda jamiyyar da ke mulkin kasar Sin mai ‘ya’yan da ta rubuta a littafi fiye da su miliyan 90, babu wata jam’iyyar siyasa da ta kai APC a yawan ‘ya’ya, balle ta fi ta yawan magoya baya a nahiyarmu ta Africa.
Saboda hangen nesa da iya tsari ne ma kwamitin rikon jam’iyyar ta APC ya nada wani kwamiti wanda zai zama mai shiga tsakani domin sasanta duk wata rigima da ka iya tasowa a cikin jam’iyyar. An ga amfanin wannan kwamitin sulhu lokacin da ya kashe wutar rigimar da ta taso a jihar Gombe tsakanin ‘yan jam’iyyar. Haka ma kwamitin ya dakile rikice-rikice a jihoshi da dama.
Wani abu da ya burge jama’a dangane da wakilan wannan kwamiti shine, wasu ‘yan son ganin rikici ya barke a APC sun so iza wutar rashin fahimta tsakanin ‘ya’yan kwamitin. Hakar su ba ta cimma ruwa ba, domin maimakon su yi rigima da juna, sai ma hadin kai ya kara karfi tsakaninsu. Wannan kuwa ya na da danganta ne da ilmi da basira da fahimtar juna wanda Allah Ya zuba a zukatan wakilan kwamitin rikon.
Idan muka koma kan wannan babban taro na ranar 26 ga watan Maris kuwa, alamu sun una za a yi shi lafiya a gama lafiya. Duk masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun nuna wa jam’iyyar kauna da girmama shugabanninta, musamman ma jagoran kwamitin rikon, Alhaji Mai Mala Buni. Allah Ya bashi baiwar hakuri da saukin kai da hikima da basira da zalaka wadanda suka bayyana, kuma suka yi tasiri a yadda ya tafiyar da aikin kwamitin.
Wannan kuwa ba abin mamaki ba ne domin Alhaji Mai Mala Buni ya san jamiyyar APC ciki da waje, har ma da yadda aka kafa ta. Ya na daya daga cikin wadanda suka yi wa jamiyyar reno mai kyau har ta bunkasa ta yi karfin da ta ci zabe sau biyu. Ya yi mata wannan reno ne lokacin da ya rike mukamin sakataren jamiyyar na kasa kafin jama’ar jihar Yobe su kira shi gida, su tsaida shi takarar mukamin gwamnan jihar wanda ya ci cikin sauki.
Salisu Na’inna Dambatta ne darektan yada labarai na APC na kasa.