Related Articles
Imrana Abdullahi
Wani sanannen Malamin addinin musulunci da ke cikin garin Kaduna Shaikh Umar Hashim, ya bayyana babbar hanyar da za a samu nasarar kawar da Cutar Korona bairus ita ce a koma ga Allah Madaukakin sarki.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a kaduna inda ya ce ta yaya za a samu nasarar kawar da Cutar Korona ba tare da an koma ga Allah ba, kuma hanyar komawa ga Allah ita ce a je masallaci kuma ga shi an kulle masallatai.
” Ko a kasashen duniya ma wannan cutar suna ta kokarin yaki da cutar Korona saboda ingantuwar kasarsu, an samu wadansu da ke son yin harkokinsu na Coci aka nemi hanasu amma nan take suka ki hanuwa sai da suka yi don haka me yasa sai mu kawai”.
Ya ci gaba da cewa jarabawa ce ta samu duniya, don haka ya dace a daina zantawa kamar yadda Allah ya ce masallaci bakinsa ne saboda haka dole ne a koma gare shi a samu sauki, ta yaya za a rufe masallatai da Coci Coci ace ana son ganin daidai.