Home / Labarai / Bafarawa Ba Shi Da Alaka Da Ta’addanci – Dokta Shinkafi

Bafarawa Ba Shi Da Alaka Da Ta’addanci – Dokta Shinkafi

Mustapha Imrana Abdullahi
An bayyana tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Dokta Attahiru Dalhatu Bafarwa da cewa ba shi da hannu ko wata alaka da duk wani aikin ta’addanci ko ta’addancin kansa balantana masu yin sa a ko’ina suke.
“Bai ta ba goyon bayan ta’addanci ba kuma babu abin da ya hada shi da masu yin Ta’adda, don haka abin da ake yadawa a cikin wadansu jaridun yanar Gizo da dandalin Sada zumunta na yanar Gizo cewa wai wanda aka kama da laifin Ta’adda ya na samawa yan Ta’adda kaya musamman takalma da kuma duba lafiyarsu wai dan uwan Bafarawa ne, hakika wannan ba gaskiya ba ne”
Bayanin Karyata wannan bayanin ya fito ne daga bakin Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, inda ya ce ai wanda aka kama da ta’addanci dan tsohuwar kamarawa ne don haka babu abin da ya hada shi da Bafarawa
” kalaman da Bafarawa ke yi a kafafen yada labarai game da illar da yan Ta’adda da ta’addancin ke yi wa Arewa babu mai iya yin irinsu sai shi Bafarawan kawai don haka ba abin da ya hada shi da masu aikata ta’addanci, kuma wannan da aka kama ba abin da ya hada tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Dokta Attahiru Dalhatu Bafarawa da wanda aka kama da Ta’adda.
Suleiman Shinkafi ya ci gaba da cewa kalaman fadin gaskiya da tsohon Gwamnan Sakkwato ke yi na fadin gaskiya babu mai iya yin irinsu, don haka ba za a siyasantar da rayukan jama’a ba haka kawai.
” mun san wadannan kalamai ba su da alaka kuma ba ta inda za su samu alaka kwata kwata, sannan shi kashin kaji akwai inda za a shafa shi ya tsaya amma duk mai son shafawa Bafarawa kashin kaji ba zai taba yuwuwa ba domin in mai fadi wawane to masu saurare ba wawaye ba ne don haka baki daya Akidar Bafarwa ta ta allaka ne a kan batun ceton Arewa da ceton talakawan Arewa da duk yadda zai yi ya ceto yan uwansa mutanen Arewa kawai, saboda haka batun alakanta Bafarawa da wannan taron ba ta ma ko taso ba domin ba mu san shi ba kuma ba mu tare da shi kuma ba mu hudda da shi ba mu san inda ya fito ba sam kuma ba mu san aikinsa ba”, inji Dokta Shinkafi.
Ya kara da cewa kowa ya Sani Dokta Dalhatu Baarawa, dan Bafarawa ne cikin garin Bafarawa, shi kuma wannan yaron dan kamarawa ne kuma tsohuwar Kamarawa ba wai sabuwar kamarawa ba ma don haka ba su da wata alaka domin bai san shi ba baki daya
Kuma abin da ya dace shi ne a kira yaron a tambaye shi ko ya san Bafarawa sai dai kawai ya rika jin sunansa kawai na Bafarawa amma bai san shi ba ba kuma wata alaka ta kusa ko ta nesa”, inji Dokta Shinkafi.
Maganar gaskiya shi ne muna kokarin sanar da jama’a ne cewa mu ba za mu amince a Sanya wa Bafarawa kashin kaji ba domin bai ji bai gani ba.
Saboda haka muke yin kira a gare shi da ya ci gaba da yin yaki na taimakawa al’umma baki daya musamman na al’ummar Arewa.
Ba da jimawa ba mun hadu tare da shi kansa Bafarawa muka ta fi majalisa muka kai kundi muna neman lallai a biya yan Arewa diyyar asarar rayuka da dukiyar da aka yi masu domin yan kudu sun ce a ba su kudi naira biliyan daya, sai mu kuma muka nemi a ba mu naira biliyan Bakwai (7) don haka duk kokarin da Bafarawa yake yi shi ne ya Ceci al’ummar arewacin Najeriya ta kowace fuska.
“Hakan ta Sanya a yanzu na zo Legas domin in kare wannan kundin da muka rubuta wa kwamitin ( fanel) da aka Sanya na batun rikicin kawo karshen rundunar yan Sanda ta SAS da aka yi a kwanan baya.
Muna kuma yin kira ga masu neman alakanta Bafarwa da wani abu can daban su daina saboda ba za su ci nasara ba  ko kadan.
“Shin wai tambaya a nan shi ne yan uwa nawa Bafarwa ke da su duk dole sai ya san abin da suke aikatawa? Amsa a nan shi ne ba zai yuwu ba sai ya san hakan, kuma shi wannan da ake yi masa tambayoyi bai ambaci Bafarwa, ko Garkuwa ko wani sunan da ya alakanta shi da wannan mutum ba don haka duk zancen banza ne kawai na neman yin batanci kawai”, inji Dokta Suleiman Shu’aibu Shinlafi.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.