Home / MUKALA / Ai Zamfarawa Ba Wawaye Bane!!!

Ai Zamfarawa Ba Wawaye Bane!!!

 

Ina mai rantsuwa da Allah, wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi kadai! Kowa yasan cewa a baya, alummar jihar Zamfara baki daya sun shiga cikin garari, da tashin hankali, da rudu, da hayaniya, da rashin tabbas, da damuwa iri-iri, kala-kala, daban-daban, a karkashin wani tsohon gwamna, mai girman, mai fadin rai, mutakabbiri, barawo, macuci, azzalumi, amma duk suka daure, suka yi hakuri, suka mika lamarin su zuwa ga Allah, basu kai kukan su wurin kowa ba, suka yi ta addu’a da rokon Allah ya kawo masu mafita. Kwatsam, sai Allah ya kawo masu mafita, ya kawo masu Gwamna Matawalle zabin Allah.

Kuma bawan Allah nan, wallahi, duk duniya ta shaida, yana iya kokarin sa, kuma yana fadi-tashi, ba dare ba rana, wurin ganin cewa, jihar Zamfara da al’ummar ta baki daya, sun samu zaman lafiya da ci gaba mai dorewa, mai albarka, kuma mai amfani. Amma duk da haka, wasu shedanu, wadanda Allah ya debe wa albarka, masu bakin uwa, har kullun, kokari suke yi su ga cewa, wai bai samu nasara ba. Kuma wai su duk suna yin wannan ne da sunan adawar siyasa!

Eh, gaskiya ne, a kowa ce jiha, cikin jihohin da ke fadin tarayyar kasar nan, ana yin adawar siyasa, amma mai ma’ana, wadda za ta taimaki jihar da kuma al’ummomin su, amma mu a jihar Zamfara, dabanci da jahilci ake nunawa karara, da sunan adawar siyasa! Adawar siyasa suke yi, wadda zata cutar da Zamfarawa da al’ummar ta, duk da sunan adawa!

Duk wahalhalun da al’ummar jihar Zamfara suka sha a karkashin mulkin fir’aunancin su, basu gani ba.

Wai su a yau har suna da bakin da zasu ce wai harkar sufuri ta shiga garari a mulkin bawan Allah, Gwamna Matawalle!

Duk wani alkhairi na bawan Allah nan wallahi basu ganin shi, kawai su kokarin su shine, suyi ta kwakule-kwakulen sharri, tare da kirkiro sharri, kazafi, da karya akan gwamnatin Matawalle, zabin Allah!

Wallahi duk abun da kuke yi muna sane, kuma wallahi duk wani makirci da kulle-kullen da kuke yi, da kisinsina akan gwamnatin jihar Zamfara muna sane da shi!

‘Yan iska, ‘yan turowe, ‘yan daba, marasa aikin yi, da kuka dauka kwangila, kuka ajiye su a hotel daban-daban, a Abuja da Kaduna da sauran wurare, kuka dauki nauyin su, kuka basu aikin yin rubuce-rubucen karya da na batanci a social media, game da gwamnatin Matawalle, duk muna sane, kuma da ikon Allah ba zaku ci nasara ba, zaku bata lokacin ku, kuma zaku yi a banza. Domin shi Gwamna Bello Matawalle da Allah ya dogara, ba zai yiwa kowa sharri ba, ba zai yaudari kowa ba, kuma ba zai ha’inci kowa ba, amma duk mai nufin sa da sharri, zai kare kan sa, ta hanyar yiwa Zamfarawa abun da ya dace, wanda zai taimakesu, tare kuma da kai karar duk wani makiri wurin Allah, mai kowa mai komai!

Kuma da ikon Allah, Zamfarawa suna tare da Gwamnan su, Muhammadu Bello Matawalle, suna yi masa addu’o’i, kuma ba zasu gajiya ba, ba zasu gushe ba, ba zasu yi kasa a gwiwa ba, wurin bashi goyon baya, da yi masa addu’o’i, da yi masa fatan alkhairi, da kuma rokon Allah akan ya gama lafiya, kuma har ya zarce, ya kara wasu shekaru hudu, da ikon Allah!

Wannan shine amsar mu akan duk wani shedani, munafuki, makaryaci, wanda aka ba wa kwangilar yada sharri da karya, game da Zamfara da al’ummar ta, da kuma gwamnatin Gwamnan Zamfarawa, Matawalle, zabin Allah, a social media!

Wassalam

Imam Murtadha Muhammad Gusau

Lahadi, 03/10/2021

08038289761

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.