Home / Labarai / Ban Taba Ganin Mai Kokarin Inganta Rayuwar Jama’a Kamar Bello Kagara Ba – Sardaunan Daneji

Ban Taba Ganin Mai Kokarin Inganta Rayuwar Jama’a Kamar Bello Kagara Ba – Sardaunan Daneji

Ban Taba Ganin Mai Kokarin Inganta Rayuwar Jama’a Kamar Bello Kagara Ba – Sardaunan Daneji

Mustapha Imrana Abdullahi

Sardaunan Danejin Katsina Alhaji Sabi’u Sa’idu Mahuta ya bayyana nadin sarautar Sarkin Yakin Danejin Katsina a matsayin abin da ya dace.

Sardaunan Danejin Katsina ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.

Ya ci gaba da cewa “Hakika abin da Danejin Katsina ya yi na Nadin Sarkin Yakin Danejin Katsina abu ne da ya dace, domin babu abin da za a bashi kamar wannan sarautar ta Sarkin Yaki, ban ta ba ganin wanda a baki dayan rayuwarsa burinsa shi ne ya taimaki rayuwar dan Adam kamar Alhaji Bello Kagara ba, domin shi baki dayan rayuwarsa koda Bacci yake yi hakika mafarkinsa na kokarin yaya zai taimakawa jama’a kamar yadda na san shi koda yaushe ta yaya zai taimakawa jama’a”, inji Sardaunan Danejin Katsina.

Ya kara da cewa “Wasu na ganin cewa idan aka ce Sarkin Yaki kamar ana yaki ne to a yanzu kuma ba lokacin yaki ba ne, abin da lamarin ke nufi shi ne mutum ne da babu abin da ya Sanya a gaba sai taimakawa jama’a tun daga can kasa har zuwa sama, ma’ana tun daga mutanen kauye zuwa ga na cikin birane a ko’ina suka samu kansu a fadin duniya baki daya”.

Don haka nadin da Danejin Katsina ya yi wa Sarkin Yaki ya cancanta, saboda an yi wa wanda ya dace domin nagartarsa da kokarin aikinsa.

“Ban yi tsammanin akwai abin da Danejin Katsina ya yi ba kamar bayar da wannan sarauta ta Sarkin Yaki ga Alhaji Bello Kagara, na so ace ba ni ne nake wannan jawabin ba saboda wasu za su yi wa magana da wata fassara daban, amma duk da haka a gaskiya ban ta ba ganin mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa baki daya wajen taimakawa rayuwar wasu ta inganta kamar Alhaji Bello Kagara, awa Ashirin da hudu hidimar sa kenan kawai taimakon rayuwar jama’a yadda za su ci gaba”.

“Domin shi zai iya taimakawa har wanda baya kaunarsa don haka idan da wannan sarautar ta Sarkin Yaki za ta yi magana hakika za ta tabbatar da cewa ta samu ainihin gidan ta inda ya dace ta zauna”.

Saboda haka za mu iya cewa Danejin Katsina Alhaji Bello Abdulkadir Yammama ya nada sarauta a inda ta dace ta Sarkin Yakin Danejin Katsina.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.