Home / KUNGIYOYI / Bamu Amince Da cire Albashin Da Jihar Kaduna Ta Aiwatar Ba – NLC

Bamu Amince Da cire Albashin Da Jihar Kaduna Ta Aiwatar Ba – NLC

Imrana Abdullahi
Kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar kaduna karkashin jagorancin kwamared Ayuba Suleiman, ta bayyana a fili cewa ba su amince da batun cire albashin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi ba.
Kwamared Ayiba Suleiman, ya shaidawa taron manema labarai a kaduna cewa ba za su amince da irin yadda Gwamnatin Jihar kaduna ta karya dokar cirar kudin ma’aikata ba, saboda Gwamna ko Gwamnati ba wanda keda izinin cirewa ma’aikata kudi haka kawai ba tare da an bi tsarin da dokar aiki ta tanadar ba.
Saboda ” sai dai wani babban ma’aikaci daga ma aikatar kwadago ta kasa ko kuma babban taron yayan kungiyar kwadago su kawai keda izinin cirewa ma’aikata Albashi amma ba haka kawai kai tsaye ba ko wani ko taron wadansu mutane  duk ba su da izinin cirewa ma aikata albashi”.
Ayuba Suleiman ya ci gaba da cewa a kwanan baya an yi taro da shugabar ma’aikatan Jihar Kaduna kuma a taron an bayyana cewa ma’aikata sun amince su taimakawa kokarin Gwamnati na tallafawa marasa karfi a cikin al’umma da kashi biyar daga albashinsu amma ba irin yadda Gwamnatin ta cire kashi 25 daga cikin albashin ma’aikata ba, haka kawai.
Amma daga baya kawai sai muka wayi gari da batun cire Albashi ba tare da wani yin cikakken tsari ba.
Don haka bamu amince ba kuma muna kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta hanzarta daukar matakin daina wannan cire ciren albashi.
Zamu dauki matakin da ya dace da dokar kasa a kan wannan batu, kuma muna kiran ma’aikata da su ci gaba da natsuwa suna biyayya ga doka domin shugabancin kungiyar kwadago na kan aikin lallai sai an dawo da kudin sa aka cirewa ma’aikata.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.