Home / Lafiya / Bamu Amince Da Nadin Sarkin Yarbawan Doka Ba – Masarautar Zazzau

Bamu Amince Da Nadin Sarkin Yarbawan Doka Ba – Masarautar Zazzau

Mustapha Imrana Abdullahi
Majalisar masarautar Zazzau ta bayyana cewa ba ta amince da wani nadin da aka yi wa Mista Isiaka Asalaye a matsayin Sarkin Yarbawan Doka a karkashin Gundumar Doka cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa ba a Jihar Kaduna.
Bayanin hakan ya fito ne daga ofishin yada labarai na majalisar masarautar Zazzau.inda ta tabbatar da cewa babu wani batun an yi wa wani nadin sarautar Sarkin Yarbawan Doka, saboda haka sai masarautar Zazzau ta yi kira ga dukkan hakimai da su daina yin irin wannan a makarantunsu saboda haka wannan nadin tuni aka warware shi sam ba shi ba alamaunsa Baki daya.
Majalisar Masarautar ta bayyana cewa an jawo hankalinta ne bisa wani nadin da aka ce an yi wa wani Mista ISIAKA ASALAYE, a matsayin Sarkin Yarbawan Doka cikin Gundumar Doka,kuma an yi taro a makarantar kwalejin Adeyemo, da ke Titin Katsina duk a cikin garin na Kaduna domin shagalin nadin sarautar Sarkin Yarbawan Doka.

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.