Home / Ilimi / Ya Dace Mutane Su Rika Yi Dai- dai Ruwa Dai Dai Tsaki – Masari

Ya Dace Mutane Su Rika Yi Dai- dai Ruwa Dai Dai Tsaki – Masari

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya yi kira ga daukacin al’umma da su rika gudanar da al’amuran rayuwa tare da fahimtar cewa akwai bukatar sadaukarwa domin samun ci gaba.
Masari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta gidan Talbijin na “Trust TV” inda ya ce ya dace mutane su Sani cewa akwai bukatar jama’a su Sani cewa akwai bukatar a rika sadaukarwa.
Gwamna Masari ya ci gaba da cewa idan dai akwai yawan mutane akwai kasuwa idan kuwa akwai kasuwa to ba shakka akwai kudin haraji sosai don haka akwai ci gaba kwarai.
“Ya dace ko dai Gwamnatin tarayya ta Sani cewa akwai bukatar a ba Jihohi dama a cikin kundin tsarin mulki damar su dauki mataki a kan matsalar tsaro ko kuma ta tashi haikan a yi maganin wannan matsala”, inji shi.
Ya kara da cewa yawan jama’ar da suke a can shekarun baya yawan jama’ar yanzu ya fi na can baya yawa nesa ba kusa ba.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.