Home / Labarai / Bamu Ga Wanda Ya Yi Kama Da Sardauna Ba A Arewa – Fasto Buru

Bamu Ga Wanda Ya Yi Kama Da Sardauna Ba A Arewa – Fasto Buru

Bamu Ga Wanda Ya Yi Kama Da Sardauna Ba A Arewa – Fasto Buru
Mustapha Imrana Abdullahi
Sanannen Malamin addinin Kirista da ke cikin garin Kaduna Fasto Yohanna Y D Buru, ya bayyana yankin arewacin Nijeriya a matsayin wurin da ya rasa tsantsar shugabannin da za su Bogi kirjin cewa sun Gaji marigayi Sardaunan Sakkwato.
Fasto Yohanna Buru ya bayyana hakan ne a wajen taron walimar cin abincin rana da ya shirya wa manema labarai a cibiyar su ta kasa reshen Jihar Kaduna.
Fasto Buru ya ci gaba da cewa ta yaya za a ce a kullum sai kashe jama’a ake yi a yankin arewacin Nijeriya, amma kamar babu wadanda za su iya yin magana har wannan matsalar ta kawo karshe.
“Shin a yanzu idan marigayi Sardaunan Sakkwato na nan shin da wane idanu za su kalle shi”.
Buru ya ce a kowane shekara ya dauki alkawarin shiryawa manema labarai irin wannan walimar cin abincin rana ne saboda kokarin da suke da shi a cikin al’umma don haka ya zamar mini dole in rika tunawa da kokarin yan jaridakuma har yanzu Allah bai gajiyar da ni ba”.
“Muna kiran jama’a da su zauna lafiya da junansu domin samun ci gaban kasa tare da al’ummarta baki daya”.
Taron dai ya samu halartar jama’a daga ciki da wajen Jihar Kaduna baki daya da suka hadar da shugabannin tabbatar da tsaro a tsakanin al’umma na masu zaman kansu, shugabannin jama’a ta bangaren iyayen kasa Sarakuna da ya samu halartar wani mutum daga masarautar Fatiskum Jihar Yabe da kuma shugabancin masu fama da Nakasa.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da dimbin manema labarai, Yan Kasuwa, Dalibai tare da wakilcin kungiyar yan jarida ta kasa duk sun samu halarta ne kamar yadda suka bayyana domin tabbatar da samun zaman lafiya.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.