Home / Kasuwanci / Masu Sana’ar Sayar Da Mota Na Bukatar Tallafi – Na brazil

Masu Sana’ar Sayar Da Mota Na Bukatar Tallafi – Na brazil

Masu Sana’ar Sayar Da Mota Na Bukatar Tallafi – Na brazil
Mustapha Imrana Abdullahi
An bayyana masu sana’ar sayar da motoci da cewa mutane ne masu bukatar tallafin Gwamnati a dukkan mataki.
Shugaban kungiyar masu sayar da motoci ta kasa reshen Jihar Kaduna Alhaji Ahmad Nabrazil ne ya yi wannan kiran a Kaduna.
Ahmad Nabrazil ya ci gaba da bayanin cewa idan mutum yana daga nesa da masu sana’ar sayar da motoci, sai aga kamar ba su bukatar tallafin Gwamnati don haka yakamata Gwamnatin ta duba sosai domin samar da tsarin yi wa masu sana’ar mota Tallafi kamar yadda ake bayar da tallafin ga masu sana’o’i daban daban  fadin Nijeriya baki daya.
” Sai mutum ya ci sannan zai iya Tallafawa wani ko wasu don haka Gwamnati ta Sani masu sana’ar sayar da motoci suna da bukatar tallafin Gwamnati kwarai”.
Ya kara da cewa idan Gwamnati ta waiwayi masu sayar da motoci kuma suka matseta hakika za ta gane cewa masu sana’ar sayar da mota na da bukatar tallafi.
” Masu sana’ar sayar da mota sun dauki jama’a da dama aiki wanda tun asali wajibin Gwamnati ne amma masu sana’ar sayar da mota sun dauke mata, saboda haka ya zama wajibi ga Gwamnati ta mika hannunta ta tabbatar da bayar da Tallafi ga masu sana’ar sayar da motoci.
Ahmad Nabrazil ya kuma yi kira ga yayan kungiyar masu sayar da motoci a ko’ina suke da su ci gaba da kiyaye dokokin da aka shimfida domin dakile cutar Korona da ta zamowa duniya annoba, kasancewar cutar ana iya daukar ta ne ta hanyar wanda ke dauke da ita yana iya yadawa wani ko wasu, saboda haka kula da lafiya ya zama wajibi.

About andiya

Check Also

APC National Chairman, Ganduje Commissions Road Named After Him in Gombe

  …Lauds Governor Inuwa’s Examplary Leadership …Says “President Tinubu, APC Leadership Proud of Gombe Governor’s …

Leave a Reply

Your email address will not be published.