Home / Lafiya / Bamu San Inda Kafar Yada Labarai Ta Channels Ta Samo Bayanin ta Ba – Zamfara

Bamu San Inda Kafar Yada Labarai Ta Channels Ta Samo Bayanin ta Ba – Zamfara

Daga Imrana Abdullahi
Sabanin irin yadda kafar yada labarai ta gidan Talbijin ta channels ta rika yada labarin cewa Sarkin Kauran Namoda Alhaji Ahmad Muhammad Asha, ya rasu ne sakamakon cutar Covid – 19 da ake kira Korona.
Faruwar wannan lamari na yada labarin mutuwar da kuma danganta lamarin na Cutar da ke addabar duniya a halin yanzu yasa wakilinmu ya tuntubu bangaren Gwamnatin domin tabbatar da wannan labarin da kafar yada labarai ta channels, ta yayata wa duniya.
Wata majiya mai tushe ta tabbatarwa da wakilinmu cewa suma haka nan suka ga irin wannan bayani a kafar Talbijin ta Cahnnels, amma ba su san inda suka samu labarin ba domin bayan rasuwar Sarkin na Kauran Namoda an dai dauki samfurin jininsa kuma har yau ba a kawo masu sakamakon Gwajin da aka yi wa Sarkin ba. Amma sai kawai suka rika ganin labarin cewa wai Sarkin ya rasu ne saboda Cutar Covid – 19.
Majiyar ta ci gaba da bayanin cewa ” A gaskiya ko wadancan bayanai da ita hukumar kula da yaki da yaduwar cututtuka ta bayyana cewa an samu wata mata da cutar a Jihar wai har da batun daga Legas aka dawo su a matakin wannan Jiha ta Zamfara ba su da labarin komai kuma ba a gaya masu ba sai dai kawai yana cewa wai an samu mai cutar a Jihar.
To jama’a yaya kuke kwallon wannan lamarin duk da cewa ba daidai bane a bayyana sunan wanda ya kamu da cuta domin ya sabawa ka’idar aikin lafiya, sai dai in shi ne ya bayyana da kansa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.