Home / Kasuwanci / Bankin Nexim Ne Kan Gaba Wajen Tattalin Arzikin Nijeriya – Nicholas

Bankin Nexim Ne Kan Gaba Wajen Tattalin Arzikin Nijeriya – Nicholas

 

 

Imrana Absullahi

 

 

Nicholas Mshelia, wani masani ne mai aikin bayar da shawara da kuma fitar da kaya kasashen waje da ya yanzu yake fitar da Kahon shanu zuwa kasashen waje ya bayyana Bankin Nexim a matsayin wanda ke kan gaba wajen bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.

 

 

Nicholas ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron bita na kwana daya inda aka yi wa jama’a masu harkar masana’antu da kuma saye da Sayarwa irin romon da ke tattare da fitar da kaya da kuma shigowa da su cikin Nijeriya da Bankin Nexim ya shirya a Kaduna.

 

 

Nicholas ya ce hakika Bankin Nexim na a kan gaba wajen bunkasa tattalin arzikin Nijeriya musamman ta fuskar shigowa da kuma fitar da kaya zuwa kasashen waje.

 

 

Ya ci gaba da bayanin cewa “wannan Bankin na kokari kwarai wajen batun kayan da suke ba albarkatun Man fetur ba, wato dukkan albarkatun Gona da sauran abubuwan amfanin gudanar da rayuwa na yau da kullum, wanda dalilin hakan ne ya sa muke kokarin fitar da albarkatun da ake samu musamman fita da Kaho zuwa kasashen waje kuma hakan na kawo amfani kwarai ga kasa da jama’arta wanda a da can zubar da shi ake yi a Bola domin babu mai so amma a yanzu muna samun albarka kwarai”. Inji Nicholas Mshelia.

 

 

A cikin abubuwan da muke fitarwa a kamfanin “N – Pizer Investment” zuwa kasashen waje sun hada da Kaho na Shanu zuwa kasashen asiya da tarayyar Turai musamman Faransa, a da can mun wayi gari Kaho idan kaje Mahauta sai dai a kwashe su a zubar, amma a yanzu ya zama ana nemansa ruwa a jallo a duk fadin duniya.

 

 

Duk inda ake bukatar Kahon a duniya za su baka irin wanda suke bukata yadda suke so, amma mafi yawa farare ake bukata kuma Dogaye ba kanana ba saboda su na yin abubuwa da yawa irinsu Tukwane, kayan botun da dai sauran abubuwa da yawa na amfanin yau da kullum abin da ake yi da Kaho kenan.

 

 

Ya kara da yi wa manema labarai bayanin cewa, masu magana na cewa da rashin Sani ne kaza ta kwana kan Dame, amma idan akwai Sani kuma ana bincike ga dan kasuwa mai binciken na’urar yanar Gizo ta zamani zai san me ake ciki domin mutum zai gane abin da ake bukata a cikin duniya.

 

 

Wani lokaci za a tambaye ka ne ace zaka iya samun wannan? domin am sanka daman kana fitar da wadansu kayan daban. Amma a wani lokacin kuma Kaine idan ka hau yanar Gizo zaka buga ka gani duk zai fito maka to, mu a na mu an neme mu ne ko zamu iya kawowa? har ma muna dauka mun aikata kuskure a farko saboda mun dauki Bakake da yawa a farko don mun dauka Kaho Kaho ne ashe Kaho ba Kaho ba ne.

 

 

Sai aka soma warewa aka ce ga irin wanda ake bukata saboda haka a yanzu muna zuwa wurare da dama mu sayi Kaho irin su Kaduna, Sakkwato, Yola, Mubi my saya mu kuma tara idan sun taru sai mu ta fi da su kasashen da ake bukatar su.

 

 

Nicholas Mshelia, ya ce kasancewar Jihar Borno wurin da ake samun Shanu masu fararen Kaho ya sa a yanzu muna da babban wurin tara Kaho a Borno kuma ba Borno kadai ba har daga kasar Kamaru ana kawo mana Kaho da muke diba, sai sun tananan shi sannan su kawo mana, don haka ne duk inda muka ji akwai sai kawai mukan je mu nema don yanzu ba mu iya samar da adadin yawan da ake bukata ba su haduwa sam, saboda haka duk inda aka ce akwai sai mu bi mu saye shi.

 

 

Ya bayyana irin yadda aka fara sana’ar neman Kaho da cewa kamar yadda aka fara ne da yan kwankwani ne da a tun farko su na zuwa Bola ne wato Jujin zubar da Shara suna diban Bolar, sai a rika kiran su mahaukata amma a yanzu ko su ma sai ka bi layi kafin ka samu. Ko su mahautan ma da yan babbakar ma sai ka bi layi ka yi bukin ka rike jari sosai domin wasu sai mun biya kudin shekara guda sannan, in kaje kuma idan wani ya rigaka sai ka jira an kammala bashi nasa baki daya sannan kai da ka zo daga baya ka samu. Yanzu haka mahautan mu na Arewa duk sun san hakan, ba su dai san inda akar kaiwa ba amma duk sun san ana bukatarshi.

 

 

Nicholas ya bayyana tsarin Bankin shigowa da kaya da kuma fitar da kaya kasashen wajen na Bankin Nexim sabanin wasu Bankunan da za su ce maka sai ka biya kudin riba na kashi 28 amma shi Bankin Nexim bai wuce Kawhi biyar (5) ba kaga akwai sauki kwarai.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.